Ƙwararru sun yi kira ga mutane da su riƙa yawaita cin gwaza wato walaha cewa yana da matuƙar amfani a jikin mutum.
Bincike ya kuma nuna cewa ganyen gwaza na dauke da sinadarin kawar da cututtuka kamar makanta,daji,hawan jini, da sauran su.
Za a iya amfana da wannan abinci ne idan aka dafa gwaza ko kuma ganyen a matsayin abinci ko kuma a yi miya da shi.
A arewacin Najeriya kuwa akan dafa gwaza domin a cinn shi haka nan, ko da manja ko man gyada ko kuma miya.
1. Ganyen walaha na dauke da sinadarin ‘Vitamin C’ wanda ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka.
2. Yana kare mutum daga kamuwa da cutar daji ta kowace iri.
3. Yana ragewa da kare mutum daga kamuwa da cutar siga ‘Diabetes’.
4. Ganyen walaha wato gwaza na dauke da sinadarin ‘Vitamin A’ wanda ke kara karfin ido sannan da kare ido daga kamuwa da cututtuka kamar su yanar ido,amosanin ido, makanta da sauran su.
4. Yana taimakawa wajen nika abinci, kawar da ciwon ciki sannan da hana yawan yin bahaya.
6. Yana hana fatar mutum tsufa da sauri sannan da kawar da cututtukan dake kama fata.
7. Yana ƙara ƙarfin jijiyoyin jiki
8. Ganyen walaha na kere mutum daga kamuwa da hawan jini
9. Yana dauke da sinadarin ‘Calcium’ wanda ke kara karfin ƙashi.
10. Ganyen walaha na dauke da sinadarin ‘Folate’ wanda ke inganta girman dan dake ciki sannan da hana mace mai ciki kamuwa da hawan jini
11. Yana kara jini a jiki musamman ga yara kananan.
12. Kara kaifin kwakwalwar mutum musamman wajen hana mantuwa.
13. Yana inganta maniyi a jikin maza.
Discussion about this post