Dalilin zargin mu na goyon bayan Boko Haram –Kungiyar Red Cross

0

Jami’in Yada Labarai na Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC) da ke Abuja, Aliyu Dawabe, ya bayyana cewa kungiyar su ba ta da nuna tausayi, goyon baya ko jinkai ga kungiyoyin ta’addanci, cikin har da Boko Haram.

Kungiyar ta Red Cross na daya daga cikin kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan agaji a yankin Arewa maso Gabas inda Boko Haram ya kassara.

Dawabe ya ce mafi yawan ‘yan Najeriya ba su fahimci yadda ayyukan Red Cross ya ke ba.

Ya ce da ya ke ayyukan Red Cross ya na tafiya ne kamar yadda Dokar Gudanar da Ayyukan Jinkai ta Duniya ta shimfida, sai wasu da dama ke ganin tunda Red Cross ba ta goyon bayan kowane bangare, to kamar ta na mara wa masu ta’addanci baya kenan.

Daga nan sai ya ce ita kuwa wannan doka, ta bayar da umarnin cewa masu aikin agaji su gudanar da ayyukan ceto ga dukkan bangarori biyu masu fada da juna.

Kafin wannan dai, Kungiyar Red Cross ta sha fama da suka da caccaka cewa ta na nuna tausayi ga Boko Haram, wadanda aka ce ta na ba su magunguna da kuma gudanar da ayyukan duba lafiyar su.

Da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES a wajen wani taro a Maiduguri, ya ce ana zargin Red Cross ne saboda ba a fahimci aikin kungiyar ba. Amma dai ya ce su ba su taimakon wadanda ke yakar junan su.

“Mu abin da mu ka fi maida kai shi ne mu yi kokarin nuna wa bangarorin da ke fada da juna cewa su mutunta dokar yaki. Wato kada su kai wa kananan yara da dattawa hari. Kada su kai wa asibitoci da makarantu da sauran wuraren ibadu hari. Kuma mu na wannan kokarin, har ma a cikin sojoji mu na isar musu da wannan sako.”

“Amma fa da zaran an ce wani ya ji ciwo, to doka ta ce ya na da ‘yancin da zai samu magani ko kulawa, abinci sannan kuma akwai hakki iyalin sa su san inda ya ke da halin da ya ke a ciki.” Wannan ma aikin mu ne, amma ba wai mu rika taimaka wa wani bangare da makamai ko wani abu ba.”

Dawaba ya ce daya daga cikin kalubalen su shi ne a fahimci irin yadda ayyukan su ke tafiya.

Sai kuma ya kara da cewa aiki ne mai wahalar gaske, domin ba abu mai yiwuwa ka kirawo ‘yan ta’adda k ace su zo wurin taron da za ka nuna musu cewa ga yadda dokar ‘yancin dan Adam ta duniya ta ce a rika gudanar da yaki ba.

Sai dai kuma mu na yin matukar kokarin mu nuna wa kowane bangare cewa ya daure ya mutunta mu. A rika bari mu na isa ga al’ummar da yaki ko rikici ya lalata wa muhalli ko asibitoci ko makarantu da sauran su.

Share.

game da Author