Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ta na da shaidu sama da 400 da za ta gabatar a gaban Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, inda ta ke kalubalantar zaben da aka bayyana Shugaba Muhammadu Buhari ne ya yi nasara.
Babban Lauyan PDP, Levi Uzeugwu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke amsa tambaya daga Shugaban Kotun, Mohammed Garba.
Uzeugwu ya kara da cewa sai dai kuma idan har za su iya samun sararin gabatar da shaidu 300 daga cikin tulin wadanda su ke da su, to wannan zai iya sa su tabbatar da hujjojin da suke dauke da su da kuma sake nazarin matsayin su.
Uzeugwu ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke amsa tambaya kan cewa ya taimaka wa kotu wajen tsara tantebur din yadda kotun za ta saurari hujjoji da shaidun da lauyoyin za su gabatar.
Garba ya sanar da babban lauyan PDP da ya yi la’akari da irin tulin yawan hujjoji ko kuma shaidun da ya ce ya na dauke da su, domin kotu ta ji saukin bayar da lokacin yadda bangarori za su yi nazarin wadannan shaidu.
Bayan an ji ta bakin Uzeugwu, sai ya roki kotu ta ba shi minti 30 domin ya samu sararin tsara yadda zai rika gabatar da shaidun na sa daki-daki, da kuma yadda kotu za ta rika bin ba’asin su dalla-dalla.
Kotu ta ba shi miti 30, wanda hakan ya sa a daidai lokacin da ake wannan labari, kotun ta tafi hutu kenan na minti 30.
Discussion about this post