Kamfanin Rarraba Harken Lantarki na Najeriya (TCN), ya bayyana babbar matsalar rashin wutar lantarki da aka fara fuskanta tun daga jiya Lahadi da cewa, ta faru ne saboda jijjigar maganadisun wutar lantarki da ya afku, wanda haka ya haddasa tashin tartsatsin wuta a Babbar Tashar Lantarki ta Benin, da ke kan hanyar Sapele a Jihar Edo.
Kakakin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki, mai suna Ndidi Mbah, ta tabbatar da afkuwar wannan matsala ce a cikin wani jawabi da ta fitar a jiya Lahadi. Ta ce matsalar tashin wutar ya afku ne a Lahadi, wajen karfe 9:10 na safe.
Hakan a cewar ta ya haddasa tashin wuta a babbar tukunyar na’urorin tara karfin lantarki ta 75MX da ke yankin.
A cewar ta, karfin jijjigar wutar bayan ya haifar da tashin tartsatsin wuta, sai kuma ya rage karfin wutar da ake rabawa daga tashar tattara karfin hasken lantarki ta kasa, abin da ta ce ya janyo raguwar lantarkin da ake raba wa kamfanonin hada-hadar lantarki na cikin kasar nan.
“Saboda wannan tartsatsin wutar ya haddasa gobara a kan matattarar na’urorin tattara hasken lantarki, saboda tsananin karfin jijjigar tartsatsin.” Inji ta.
Sai dai kuma duk da dai ba ta bayyana irin tsananin karfi ko munin barnar ba, Ndidi ta bayyana cewa tuni tun a jiya Lahadi, wajen karfe 1:30 na rana aka dukufa ka’in-da-na’in ana kokarin gyara, domin dawo da wuta baki daya a kasar nan.
Sai dai kuma alamoli na nuna cewa wannan matsala da ta faru jiya Lahadi, za ta kara munana matsalar karancin haske da karfin lantarki da ake fuskanta a kasar nan.
Ita dai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta sha yin ikirarin cewa an samu karin karfin lantarki a kasar nan, daga migawats 5,000 har ya kan kai migawats 7,000.
Amma kuma jami’an TCN sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa karfin wutar kasar nan bai wuce migawats 4,000 zuwa 4,500 ba, a kowace rana.
Idan ba a manta ba, TCN ta datse wa wasu kamfanonin sayar da wutar lantarki biyu wutar da ta ke raba musu.
Duk da haka, Ndidi ta jaddada cewa TCN na nan na ta kokarin kara karfin harken lantarki a fadin kasar nan.
Discussion about this post