Atiku ya koka a kan yadda gwamnatin Buhari ke kara ciwo tulin basussuka

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya koka angane da yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ci hana da ciwo wa kasar nan tulin basussukan da ya cika mata ciki har iya wuya.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labaran sa, Paul Ibe ya fitar ranar Laraba, Atiku ya yi kira da a gaggauta kulle hancin igiyar bashin da Najeriya ke ciwowa kafin ya durkusar da tattalin arzikin kasar nan.

Atiku ya ce kafin gwamnatin PDP da ta shekara 16 a kan mulki ta sauka cikin 2015, ta bar bashin naira tiriliyan 12. Amma a cikin shekaru hudu kacal na mulkin Buhari, wannan bashi ya rubanya, kuma a yanzu haka ba a daina ciwo bashin ba.

“Wani abin tashin hankali kuma shi ne yadda gwamnatin Buhari ta sake ciwo wani sabon bashi na naira bilyan 560 tsakanin watan Disamba 2018 zuwa Maris 2019.” Inji Atiku.

Atiku ya kara da cewa bashin da aka ciwo, ba na tilsa ba ne. Ya bada misali da yadda aka ciwo bashi na kudi, aka rika raba wa jama’a da sunan ‘Tradermoni’, tsarin da Atiku ya ce siyasar kamfen ce kawai aka yi wa jama’a domin a ribbace su a samu kuri’un su.

Ya kara buga misali da yadda aka daina shirin bayan kammala zaben 2019.

“Mu na mamakin yadda ake ci gaba da kwaso wa Najeriya bashi da sunan ana gudanar da ayyuka da kudaden, alhali kasar nan har yanzu ba ta fita cikin jerin kasashen da ke fama da kuncin falauci da fatara a duniya ba. Kuma har yanzu duk da dimbin bashin da ake ciwowa, Najeriya ce a sahun gaba wajen tulin yaran da ke gagaramba a kan titi ba su zuwa makanta.”

“Wannan dabarar-rashin-dabara ce a ce kullum sai dai a ramto kudade a yi ayyuka. Sai an ciwo bashi a biya albashi. Sannan kuma kusan kashi 50 bisa 100 na kudaden shigar kasar nan ya na tafiya ne wajen biyan kudaden ruwa na wadannan basussuka da aka ciwo, ba ma wajen biyan bashin ba.”

Atiku dai ya shiga cikin sahun masu gargadin Najeriya a kan illar tulin bashin da ta ke ciwo wa al’ummar kasar nan.

Cikin wadanda suka gargadi Najeriya, Har da Bankin Bada Lamuni na Duniya, IMF.

Share.

game da Author