Wasu bayanai dan adawa Reno Omokri ya watsa a shafin san a twitter, sun nuna yadda INEC ta yi aikin loda bayanan tantance rajistar masu zabe da ga na’urar tantancewa (Smart Card Reader) zuwa cikin babbar na’urar rumbun ajiyar bayanai (server), a lokacin zaben 2019.
Takardar bayanin dai Omokri ne ya watsa su a soshiyal midiya jiya Laraba, kuma ta na kunshe ne da waru bayanai da Sakatariyar INEC ta Kasa, Rose Oriaran-Anthony ta rubuta jami’an INEC dangane da wasu kalubale da aka fuskanta wajen loda bayanan daga na’uran ‘card reader’ zuwa cikin ‘server.’
Abin da takardar bayanin ta kunsa
“Hukumar Zabe ta lura kuma ta damu kwarai ganin irin dimbin yawan ‘card reader’ da aka samu wadanda ba su dauke da bayanan tantance masu rajista a wannan zabe na shugaban kasa da na majalisar dattawa da ya gabata.”
Sakatariyar ta INEC ta rubuta wa dukkan Kwamishinonin Zabe na Kasa (REC) wannan wasika ce a ranar 25 Ga Maris, 2019.
Sannan kuma a cikin takardar, ta nuna damuwa cewa ‘card reader’ har 4,786 duk ba su dauke da wadannan bayanai bayan da aka gudanar da zaben shugaban kasa da na sanatoci a ranar 2 Ga Fabrairu, 2018.
Wadannan adadi sun nuna ‘card reader’ kashi 4 bisa 100 ne suka samu wannan matsala daga cikin adadin wadanda aka gudanar da zaben da su.
Ga wani karin bayanin
Oriaran Anthony ta kara rubuta musu cewa: “Ga shi nan ma na hadu muku da taswirar zanen adadin mazabun da aka kasa loda bayanan su zuwa rumbun tattara bayanai daga ‘card reader’ wato “ SCR backend’.”
Haka dai ta rubuta a Turance a cikin wasikar da ta aika musu, wadda Omokri wa watsa a soshiyal midiya jiya Laraba.
Daga nan sai ta umarci dukkan Kwamishinonin Zabe na Kowace jiha ya tuntubi babban jami’in gudanar da ayyukan na’urorin INEC domin ya gano dalilin da ya sa ‘card reader’ ta kasa loda wadancan bayanai a ranar zabe.
Ta kuma ba su kwanaki uku, wato zuwa ranar 28 Ga Maris, 2019 domin maido mata da amsar cikakken bayani.
Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye ya ki yarda ya amsa tambayar da PREMIUM TIMES ta yi masa a kan wannan batu.
Discussion about this post