Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kara bayar da fifiko wajen karfafa dakarun Najeriya.
Ya yi wannan alwashin ne a lokacin da ya ke jawabi wajen bikin Yaye Sojoji 187 da suka halarci kwas na 28 a Cibiyar Horas da Sojoji ta Kaduna.
A taron wanda ya gudana jiya Laraba, Osinbajo ya sha alwashin cewa “nan da shekaru kadan masu zuwa, Najeriya za ta zarce dukkan kasashen Afrika wajen yawan karfin sojoji da na makamai nesa ba kusa ba.
Daga nan sai ya kara jinjina wa sojojin Najeriya bisa irin namijin kokarin su wajen hana Boko Haram cikar burin su na kama wasu yankuna a kasar nan.
Ya nuna gwarzantakar sojojin Najeriya wajen murkushe hare-haren Boko Haram, da kuma yadda suka dakile ta’addancin su har Boko Haram din ba su iya motsawa sosai a yanzu.
Osinbajo ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a magance barazanar kungiyar ta’addanci ta ISWAP, wadda itace uwa ga Boko Haram, kuma za a kara matakan tsaron kasar nan sosai da sosai.
Sai dai kuma ya yi kira ga hukumar soja da ta fito da farfagandar yadda za ta kashe guyawun Boko Haram da a yanzu suke amfani da soshiyal midiya su na watsa bayanai na karya, domin su rika nuna wa duniya cewa wai har yanzu da sauran karfin su.
“Har yanzu akwai barazana da Boko Haram na kungiyar ISWAP, wadanda su kan su din ma ba wani karfi gare su ba a yanzu, sai dai kawai su na kai hare-hare ne na kwanton bauna a inda ake da karancin jami’an tsaro, ko kuma kai harin sari-ka-noke. Sai kuma farfagandar karya da kairayi da suke yi a soshiyal midiya, su na nuna cewa wai da karfin su daram.” Inji Osinbajo
“A matsayin ku na jami’an sojojin da ke wannan zamani na karni na 21, ya kamata ku rika fito da kan ku ta hanyar farfagandar nuna wa abokan gabar ku irin karfin da ku ke da shi. Za ku iya yin haka ta hanyar amfani da soshiyal midiya, wadda a wannan zamanin ita ma makami ce tamkar makaman yakin da ku ke amfani da su.
Sannan kuma ya ce ana ta kokarin ganin an shawo kan rikicin Fulani da manoma da sauran hare-haren da ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane ke yi.