Jam’iyyar APC ta Kasa ta soki Farfesa Itse Sagay, saboda ya nuna mamakin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Sanata God’swill Akpabio mai guntun kashi a cikin sabbin ministocin sa.
Sagay, wanda Farfesa ne a fannin shari’a kuma baban lauya, ya nuna matukar mamakin yadda Buhari ya zabi Akpabio, tsohon gwamnan Akwa Ibom ya nada shi minista.
EFCC ta zargi Akpabio da wawurar naira bilyan 108 a lokacin da ya ke gwamna tsakanin 2007 zuwa 2015.
An daina jin yadda binciken sa ya kasance, tun bayan da ya fice daga PDP ya koma APC cikin 2018.
Sagay ya yi magana a kan sa, inda ya bayyana mamakin sa kamar haka: “Wato duk a cikin sabbin ministocin da Buhari ya bada sunayen su. Akpabio ne kadai na ke tambaya da mamaki.
“Duk wanda ake zargin karkatar da kudade, bai kamata a nada shi minista ba. Amma har yau ban san dalilin da ya sa Shugaban Kasa ya zabe shi har ya saka sunan sa a cikin sabbin ministoci ba.”
Sai dai kuma APC ta maida masa martani cewa EFCC ta daina binciken sa, bayan wanda ya rubuta korafi a kan Akpabio ya kasa bayar da hujjoji.
Wani lauya ne dai a Abuja, mai suna Lawrence Akpenyong ya rubuta takardar korafi ga EFCC a bisa zargin Akpabio ya sakwartar da naira bilyan 108.
Discussion about this post