Masu Sa-ido kan Zabe daga Tarayyar Turai sun bayyana cewa manyan jam’iyyun Najeriya biyu, watau APC da PDP duk sun yi jagaliyanci da tayar da hargitsi a lokutan zaben 2019.
“Dukkan su na da hannu dumu-dumu wajen kasa kawar da tashe-tashen hankula daga magoya bayan su. Haka ita kan ta jam’iyya mai mulki wato APC, an zarge ta da yin amfani da karfin mulki a matakin gwamnatin tarayya da jihohin kasar nan.” Haka dai masu sa-idon suka bayyana a cikin rahoton da suka fitar a jiya Asabar.
Masu sa-idon daga Kungiyar Tarayyar Turai sun ce an kashe mutane 150 a rikice-rikicen da ke da nasaba da zaben 2019 a fadin kasar nan.
“Zabukan da aka gudanar sun samu fama da tashe-tashen hankula da kuma barazana da tsorararwa ga masu jefa kuri’a. Wannan kuma ya gurbata martaba da kimar da zabukan ke da shi, kuma zai iya shafar zabukan da za gudanar a kasar nan na gaba.
“An kashe kimanin mutane 150. Ita kan ta Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bada rahtannin kai hare-hare a ofisoshin ta, garkuwa da jami’an ta da kuma zargin yin lalata da wasun su har ma da sauran rikice-rikice irin su satar akwatu da kekketa sakamakon zabe.”
PREMIUM TIMES ta bada rahoton yadda aka yi tashe-tashen hankula a jihohin Benuwai, Ebonyi, Imo, Kano, Rivers da Akwa –Ibom.
An kama kalilan daga cikin wadanda suka karya dokokin zabe, saboda abin ya fi karfi jami’an tsaro.
A jihar Rivers kuwa, cikin wadanda suka rayukan su har da sojoji, wadanda suka yi fito-na-fito da matasa ‘yan ta-kife a lokacin zabe.
Tarayyar Turai ta ce su ma ‘yan jarida an ci zarafin da dama daga cikin su.
“Sannan kuma su ma masu sa-ido an ci mutumcin su an tozarta su. Cikin wadanda suka ci mutuncin na su baya ga masu jagaliyar siyasa, har ma da jami’an tsaro.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka ci zarafin ma’aikatan ta uku a jihohi daban-daban.
Ma’aikatan sun su ne Hassan Adebayo, Ebuka Onyeji da Kunle Sani.
Discussion about this post