MAKARANTAR MAKAFI TA JIGAWA: Inda dalibai suka gwammace yawon barace-barace –Jami’i

0

Mu na dauke da rahoton halin da Makarantar Makafi ta Jihar Jigawa ke ciki, inda wani jami’i ya bayyana cewa dalibai da dama suka gwamnace yawon barace-barace, maimakon makaranta.

An kafa wannan makaranta cikin 2013, da niyyar kula da ilmin yara makafi a fadin kasar nan.

An gina makarantar a garin Limawa, cikin karamar Hukumar Dutse, Jihar Jigawa. Musamman an kafa ta ne domin ilmantar da yara makafi.

Makarantar wadda ke cikin Dutse, ta na da dalibai 66 da aka fara yi wa rajista, kamar yadda mataimakin shugaban makarantar, Husseini Mahmud ya shaida.

Sai dai abin takaici, daga cikin yaran 66, guda 10 ne kadai wadanda ke zaune kusa da makarantar ke zuwa daukar darussa cikin makarantar.

Ya ce gaba daya a yanzu dalibai hudu ne a bangaren karamar sakandare, sai wasu shida a ajin firamare

DALILIN DA YA SA DALIBAI BA SU ZUWA MAKARANTAR

Da ya ke bada dalilan da ya sa yaran ba su zuwa makaranta, Daraktan Ayyuka a Hukumar Ilmin Matakin Farko, Alhassan Marke, yace:

“Mai yiwuwa saboda ganin irin kudin da masu barace-barace ke samu a cikin al’ummar mu. Ko kuma za ta yiwu saboda ko kuma watakila saboda sun fahimci babu wani makaho mai ilmi da ya tabar cirar-tuta, har ya shahara ya zama wani abu a cikin al’ummar mu. Ba na jin idan akwai cikakkun makafi goma cif da ke aiki a cikin gwamnatin jigar Jigawa.

“Babban kalubalen da makarantar ta makafi ke fuskanta, shi ne daukar dalibai. Mu dai a na mu bangaren mu na yin bakin kokarin mu, kuma ba za mu gajiya ba. Wasu makafi su na kallon makarantar kamar an kawo musu bakon abun da ba su gamsu da shi ba, wasun su kuma da dama su na yi wa kan su kallon dama haka Allah ya halicce su domin su yi bara su ci abinci a rayuwar su.”

Ya nuna damuwar sa dangane da wannan kalubale, duk kuwa da irin kokarin da gwamnatin jiha ke yi, musamnan wajen yin amfani da masu ruwa da tsaki wajen wayar wa da makafi kai domin su ma san akwai makarantar da kuma alfanun da ke tattare da ita.”

AN YI BA A YI BA: Gwamnati Ta Tara Dalibai Makafi, Amma Ba Ta Ciyar Da Su

Sai dai kuma Mataimakin Shugaban Makarantar, Mahmud, ya shaida wa manema labarai cewa duk da makarantar ta kwana ce, amma ba a tsara ta yada gwamnatin za ta rika ciyar da daliban cikin makarantar ba. duk kuwa da ya ke cewa makafi ne.

Wannan ma na daga cikin dalilin da ya sa dalibai suka daina zuwa, da yawan su suka gwamnace yawon barace-barace.

Marke ya ce makarantar na da wadatattun kayan koyar da makafi ilmi, tun daga lokacin da aka kafa ta, har zuwa yanzu. Amma daliban da ke da rajista a fadin jihar, suka daina zuwa, saboda babu tsarin ciyar da daliban. Haka Marke, mataimakin shugaban makarantar ya bayyana.

“Mu na da wurin kwanan dalibai da na malaman su. Abin da kawai watakila ya sa sauran dalibai na cikin jihar ba su zuwa makarantar, shi ne saboda gwamnati har yanzu ba ta fara ciyar da daliban ba da ke kwana a cikin makarantar.

MAKANTA BA TA HANA ILMI

Duk da wannan kalubale, PREMIUM TIMES ta samu tattaunawa da wasu matasan dalibai da suka daure a cikin wannan hali domin su ka sun samu ilmin zamani.

Maryam Adamu mai shekaru 16, ba ta gani, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an saka ta firamare cikin 2013, amma yanzu ta na aji biyu na karamar sakandare.

“Fata na shi ne na samun ilmi domin na dawo wannan makaranta na rika koyarwa. Saboda na fahimci akwai karancin malamai a wannan makaranta.”

Shi kuwa wani mai suna Ayuba Isma’il, cewa ya yi so ya ke ba zai taka burki daga neman ilmiba, har sai ya yi digiri tukunna.

Wani likitan idanu a Babban Asibitin Rasheed Shekoni da ke Dutse, mai suna Abdullahi Idris, ya shaida wa Premium Times cewa akan samu kashi 1.2 bisa 1000 na yara jirajirai makafi da aka haifa a jihar.

Ya ce kadan daga cikin dalilan da ke ana haihuwar yara makafi shi ne cutar gulokoma, yanar ido, rauni da kuma cututtukan sanyi na al’aurar mace ko namiji.

Share.

game da Author