Kwamitin binciken zargin badakalar bacewar wasu kudaden masarautar Kano da ake yi wa sarki Muhammadu Sanusi ya bada shawarar lallai a dakatar da sarkin daga ci gaba da zama a kujerar masarautar Kano.
Kwamitin ya ce ci gaba da zaman sa a kujerar sarautar Kano na kawo musu cikas a binciken da suke yi a yanzu.
Baya ga haka kwamitin ta ce ta gano wurare da dama da suke ganin sarki Sanusi ya jidi kudin masarautar ne ba tare da ya bi dokar kashe kudin masarautar ba.
Kwamitin ya kara da cewa sarki Sanusi ya barnata sama da naira biliyan 3 a tsawon shekarun da yayi yana sarautar Kano.
Shuagaban wannan kwamiti Muhuyi Magaji ne ya mika wa kamfanin dillancin labaran Najeriya kofin sakamakon Binciken da su kayi.
Binciken ya nuna cewa akwai kwangiloli da masarautar ta bada karkashin jagoranci Sarki Sanusi na gyaran Babban Daki, Kofar Kudu da Gidan Sarki Dorayi wadda duk ya ba makusancin sa ne, Mannir Sanusi.
Sannan kuma ko yadda aka ba da wannan kwangiloli ma ba a bi doka da ka’ida ba wanda shima a dalilin haka suke kira da a ruguje wannan kwangilaloli sannan a taso keyar wadanda ke da hannu a badawa da yin kwangilolin.
Rahoton binciken ya kara da cewa ba dakatar da sarkin kawai za ayi ba, muddan aka kama shi da laifi zai iya gangarawa gidan yari.