Wani kwamanda da sojoji shida sun bace bayan da Boko Haram suka kai farmaki kan sansanonin sojoji biyu a ranar Asabar. Ana kuma fargabar cewa akwai ma wani soja daya da ya rasa ran sa.
Sannan kuma an tabbatar da salwantar makamai “wadanda ba za a iya kididdgiwa ba”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa PREMIUM TMES.
Boko Haram sun kai hari ne kan sojojin Bataliya ta 192 da ke kauyen Delwa, kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, cikin Karamar Hukumar Konduga.
Sun kuma kai wani harin a kan wasu sojojin na Bataliya ta 242 da ke Karamar Hukumar Marte, kusa da Tafkin Chadi. Haka dai wata majiya a cikin sojoji ta tabbatar wa PREMIUM TIMES.
An kuma hakkake cewa hare-haren biyu an shirya su ne tsaf kafin a aiwatar da su, saboda an kai harin ne a daidai lokaci guda a Marte da Koduga din da karfe 6 daidai na yamma.
Wannan hari na ranar Asabar ya biyo bayan wani hari da aka kai makonni biyu da suka gabata, a ranar 22 Ga Mayu.
Harin dai an kai shi ne a wani sansanin sojoji da ke cikin Karamar Hukumar Gubio, Jihar Barno.
Duk da wannan hari da aka kai na ranar 22 Ga Mayu, Babban Hafsan Askarawan Najeriya Tukar Buratai, ya kara jaddada cewa an murkushe Boko Haram.
Janar Buratai yayi wannan furuci ne kwanaki biyu kafin harin Konduga da na Marte, wadanda aka kai a ranar Asabar da ta gabata.
An ce Boko Haram da suka kai wannan hare-hare na baya-bayan nan, sun fito ne dajin Alagarmo da ke cikin Karamar Hukumar Dambo.
Sun kai harin ne cike da motocin yaki hudu da kuma bindiga mai jigida, samfurin tashi-gari-barde, wadda ake kafawa a kan motar yaki har guda 12.
Sai dai kuma har yau ba a san inda wasu sojoji shida suke ba. An kuma tabbatar da kashe soja daya.
Duk da farmakin da Boko Haram suka kai, an tura karin sojoji daga Maiduguri, kimanin kilomita 30 daga wurin fafatawar.
Ksrin sojojin sun taiamaka an yi galabar sake kwato wuraren da aka kaiwa hare-haren, bayan da maharan sun gudu.
“Boko Haram sun arce motocin zabarin yaki da manyan bindigogi har guda biyu, motar daukar sojoji daya, babbar bindiga da kuma albarusai masu tarin yawa. Sun kuma banka wuta a kan wata tankar yaki samfurin T155.”
Kakakin Yada Labarai na Sojoji, Sagir Musa, bai amsa kiran neman karin bayanin da aka yi masa ba.
Discussion about this post