MAJALISAR KANO: Dan takarar gwamnati ya sha kaye

0

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zabi Abdul’aziz Gafasa a matsayin sabon Kakakin Majalisar Jiha zango na tara.

Zaben na sa ya biyo bayan bayyana takarar sa da Dan Majalisa mai wakiltar PDP daga Karamar Hukumar Dala, Lawan Hussain ya yi a jiya Litinin a lokacin zaman farko na Majalisar.

Gafasa wanda ya taba yin shugabancin majalisar a a zamanin mulkin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, ya samu goyon bayan dukkan mambobi ’yan jam’iyyar PDP su 13 da ke majalisar.

Sannan kuma ya samu goyon bayan mambobi 8 daga jam’iyyar su ta APC.

Majiya mai tushe ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa, sauran mambobin majalisa na APC su 18 duk Dan Majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Doguwa suka zaba.

Hakan ta sa Gafasa ya samu kuri’u 21, shi kuma Hon. Doguwa, wanda aka hakkake cewa shi gwamnatin jiha ke goyon baya, ya samu kuri’u 18 kacal.

An zabi mai wakiltar Karamar Hukumar Makoda, Hamisu Cigari, a matsayin mataimakin shugaba a karo na hudu.

Gafasa ya gode wa mambobin majalisa saboda zaben sa da suka yi, kuma ya sha alwashin ba zai ba su kunya ba.

Ya sha alwashin tafiya tare da dukkan mambobin majalisa duk kuwa akwai masu bambancin jam’iyya.

Ya tabbatar da cewa Majalisar Dokokin Kano za ta rika kafa dokokin da ta san za su amfani al’ummar Jihar Kano gaba daya tare da kawo musu ci gaban bai-daya.

“Za mu yi aiki tare da sauran bangarorin gwamnati domin tabbatar da ci gaban jihar Kano ta yi gogayya da manyan kasashen duniya.

“Sannan kuma za mu tabbatar da cewa Majalisa ba ta zama ’yar amshin Shata ba.”

Share.

game da Author