Abincin da ake sayarwa a titinan Lagos da Kano dauke ya ke da cututtuka -Bincike

0

Wani binciken baya-bayan nan ya tabbatar da cewa abincin da ake sayarwa a bude a kan titinan Lagos da Kano ya na dauke da cututtuka.

Binciken ya ja kunnen mazauna wadannan manyan birane biyu da su yi kaffa-kaffa daga sayen abincin da ba a cikin gidajen su suka dafa ba, wato musamman wanda ake sayarwa a gefen titina.

Rahoton binciken ya nuna cewa abincin cike ya ke da gurbatattun sinadarai da magungunan kashe kwari da tarkacen kananan karafuna da sauran su.

An kuma yi kiran gwamnatin tarayya da gaggawa ta hana talla da sayar da abinci barkatai a kan titi. Wannan inji rahoton zai rage illar cin gurbatatten abinci mai barazana ga lafiyar jama’a da dama.

An yi wannan kiran ne a ranar Juma’a a Abuja a wurin Taron Ranar Tunawa da Tsaftar Abinci ta Duniya.

Ana gudanar da taruka da jawabai a wannan rana domin jawo hankalin duniya wajen yin kaffa-kaffa da kuma kawar da abinci mai haddasa cututtuka ga jama’a.

DOKAR HANA SAYARWA DA CIN GARAU-GARAU

A yanzu haka dai akwai kudirin dokar hana sayar da abincin garau-garau barkatai a kan titi na a gaban Majalisar Tarayya ana tattauna ta.

Da ya ke jawabi a wurin taron, Wakilin Kungiyar Kula da Abinci ta Duniya a Najeriya, Suffyan Koroma, ya ce kiyaye lafiyar abinci abu ne mai matukar muhimmanci domin tabbatar da cewa an noma abinci, an sarrafa shi, an tallata shi, an sayar da shi kuma an ci shi ba tare da ya na dauke da cutar komai ba.

Koroma wanda Alphonsun Onwemeka ya wakilta, ya ce binciken abinci mai gina jiki da aka gudanar a Lagos da Kano ya nuna cewa a wadannan birane biyu ana dirkar abinci mai dauke da cututtuka, har da abincin da ke da sindaran maganin kashe kwari.

“Wannan ya kamata ya zama hannun-ka-mai-sanda ga gwamnatin tarayya domin ta gaggauta tashi haikan wajen ganin an kawar da wannan babbar barazana ga al’umma.”

Binciken ya ci gaba da cewa, cututtuka masu nasaba da sanadin abinci mai dauke da kwayoyin cuta barazana ce ga lafiya da kuma yawan matasa da manya masu iya aikin karfi.

A na sa jawabin, Babban Sakatare a Ma’aikatar Kiwon Lafiya, Abdulaziz Abdullahi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dauki barazanar gurbataccen abinci da muhimmanci.

Ya ce dalili ma kenan har ta kafa Shirin Tabbatar da Ingancin Abinci na Kasa.

Share.

game da Author