RASHIN MINISTOCI: Ga Sunayen Manyan Sakatarorin dake rike da Ma’aikatun Tarayya

0

Kwanaki 14 kenan tun bayan da Cif Jojin Najeriya Mohammed Tanko ya rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Kasa karo na biyu, daga 2010 da zai sake rike ragamar mulki har zuwa 2019.

Sai dai kuma duk da cewa Buhari ya umarci Ministocin sa su shirya takardun ajiye aiki, tun a ranar 22 zuwa 28 Ga Mayu, har yau bai nada sabbin Ministoci ba.

Idan ba a manta ba, a zangon Buhari na farko, tsakanin 2015 zuwa 2019, sai da ya shafe watanni shida kafin ya nada ministocin sa a ranar 11 Ga Nuwamba, 2019.

Da aka rika nuna damuwa dangane da jinkirin da ya yi, Buhari a lokacin ya maida raddin cewa, “ai Ministoci ba wani aiki suke yi ba, sai fa surutai kawai.”

Tun daga lokacin jama’a da dama suka fara tababar shin Buhari zai iya kamo bakin zaren matsalolin Najeriya har ya warware inda ya cukurkude kuwa?

Wannan jinkiri da ya yi ne masana tattalin arzikin kasa suka bayyana cewa na daya daga cikin dalilian da Najeriya ta afka cikin matsi da kuncin tattalin arziki a cikin 2016.

PREMIUM TIMES ta kawo musu sunayen Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da ke rike da Ma’aikatun Tarayya daban-daban, wadanda Ministoci suka damka musu ragamar tafiyar da ma’aikatu, tun bayan saukar su daga mukamin Minista makonni biyu da suka gabata:

Ma’aikatar Harkokin Sadarwa- Istiafanus Fukur

Ma’aikatar Harkokin Tsaro- Nuaratu Batagarawa.

Ma’aikatar Harkokin Ilmi- Sonny Echono

Ma’aikatar Tsaftace Muhalli- Odusote Abimbola

Babban Birnin Tarayya, FCT- Ohaa. Chinyeaka Christain.

Ma’aikatar Harkokin Tsaro- Mahmoud
Isa- Duste

Ma’aikatar Harkokin Waje- Mustapha Suleiman.

Ma’iakatar Kiwon Lafiya- Abdullahi Abdullahi

Ma’aikatar Yada Labarai- Grace Isu Gekpe

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida- Georgina Ehuriah

Ma’aikatar Harkokin- Dayo Apata

Ma’aikatar Harkokin Kwadago- Williams Alo

Ma’aikatar Inganta yankin Neja-Delta- Aminu Aliyu Bisalla.

Ma’aikatar Harkokin Fetur- Yemi Esan Folasade

Ma’aikatar Ayyuka Da Gidaje- Mohammad Bukar

Ma’aikatar Inganta Makamashi- Louis Edozien

Ma’aiktatar Kimiyya Da Fasaha- Birtus Bako

Ma’aikatar Albarkatun Kasa- Abdulkadir Muazu

Ma’aikatar Kasuwaci Da Zuba Jari- Edet Sunday Akpan

Ma’aikatar Harkokin Sufuri- Shaibu Zakari

Ma’aikatar Harkokin Ruwa- Ekaro Comfort Chukwumuebobo

Ma’aikatar Harkokin Mata- Ifeoma Anabogwu

Ma’aikatar Harkokin Matasa Da Wasanni- Olusade Adesola

Share.

game da Author