Gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa za su yi wa matsalar tsaro taron-dangi, ta hanyar kafa wani babban wanda aikin sa zai jibinci shawo kan matsalar tsaro.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamna Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya furta haka a cikin wata sanarwa da ya saw a hannu da kan sa, a Abuja.
Ya ce daga cikin shirye-shiryen har da abin da ya kira “karfafa sakateriyar Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya domin taimakawa wajen shawarwari kan tattalin arziki, shawarwari kan tsare-tsare, gudanarwa da kuma dabarun tattalin arzikin kudade.”
Sauran ajandojin da tsare-tsaren kungiyar ke shirin kafawa sun hada da tsaro, inganta kasuwanci da hannayen jari, samar da ayyukan yi, sabunta wasu dokokin kasar nan.
Ya ce gwamnonin Najeriya sun amince za su gudanar da taron ganawa na kwana daya tare da manyan cibiyoyin hada-hadar kudade, kamar su Babban Bankin Duniya da Gidauniyar Bill da Melinda.
Taron kuma zai karbi bakunci dukkan masu ruwa da tsaki a fannin tara kudaden haraji. Harv ya kara da cewa a lokacin wannan taro, shugabannin hukumar tara kudaden haraji na jihohin kasar nan duk za su hallara domin yin wato a lokacin.
Matsalar tsaro na ci gaba da dabaibaye kasar nan. A Yankin Arewa maso Gabas ana fama da Boko Haram. Jihohin Arewa maso Yamma da fama da mahara da ’yan samame su garkuwa da mutane.
Sojojin Najeriya na kan ayyukan tabbatar da tsaro a cikin jihohi 26 na fadin kasar nan.
Yayin da a cikin makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Zamfara, inda aka fi fama da ’yan bindiga, Bello Matawalle Ya lula Dubai, domin taro da wasu kwararrun shawo kan matsalar tsaro.