Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya musanta kalaman da aka rika dangantawa da shi cewa akwai rumbun ajiyar alkaluman zabe ko a lokacin da ya yi shugabancin hukumar a lokacin zaben 2015.
A cikin wani sako da aka rika watsawa kuma ana danganta shi da Jega, an ce wai ya ce ko lolacin da ya ke shugabancin INEC akwai wannan rumbun ajiyar alkaluman sakamakon zabe da aka fi sani da ‘server’.
Wannan magana ta jawo ka-ce-na-ce da ce-ce-ku-ce a cikin kasar nan, biyo bayan ikirarin da Shugaban INEC na yanzu, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi cewa babu ‘server’ din tattara sakamakon zabe a zaben 2019.
Jega shi ne ya maye gurbin Maurice Iwu a shugabancin INEC cikin 2010, kuma sai da ya shugabanci zabuka biyu kafin ya sauka, wato na 2011 da kuma na 2015.
An maye gurbin sa da shugaban INEC na yanzu, Farfesa Mahmood Yakubu, bayan da Amina Zakari ta yi shugabancin riko na dan wani takaitaccen lokaci.
YADDA OLUSOLA YA KIRA WA JEGA RUWA
Wani shafin twitter na wani mai suna Olushola Olufolabi ne mai suna @olushola_shola ya fara buga furucin da aka rika dangantawa da Jega.
Ya rubuta a shafin san a twitter cewa, Jega ya ce: “A iyar sani na INEC ta na da ‘server’, domin ko a lokacin da ina shugabancin hukumar ai sai da kuma tattara bayanan sakamakon zabe a cikin rumbun ‘server’ na intanet. Ranar wanka ai ba a boyon cibi.”
KARYA AKE YI MINI – Jega
A cikin wani sakon tes da wani hadimin Jega ya turo wa PREMIUM TIMES a madadin sa, Farfesa Jega ya jaddada cewa tun daga lokacin da ya yi shugabancin INEC har ya sauka, babu lokacin da suka taba tattara sakamakon zabe a rumbun ajiyar sakamakon zabe na intanet, wato ‘server’.
“Wannan wata karya ce ake kantara mini ko aka kitsa mini. Ban taba cewa INEC a lokaci na mun tattara bayanan sakamakon zaben ta intanet, wato rumbun ajiya na ‘server’ ba. Domin a tsarin Dokar Zabe, laifi ne a tattara sakamakon zabe ta kafar sadarwar zamani, wato ‘server.’
“Na kasa gane dalilin da zai sa wasu gafalallun mutane za su zauna su kirkiri karya a danganta ta da ni. Su ce na ce abin da ban ce ba. Saboda ban taba fadin haka ba. Karya ce kawai su ke yi.”
Haka raddin da Jega ya aiko ga PREMIUM TIMES ga wadanda ke cewa ya ce sun yi amfani da ‘server’ a lokacin da ya ke shugabancin INEC.
Sai dai kuma duk da wannan karyatawa da Jega ya yi, wannan rikita-rikita za ta dade ana tattaunawa kan ta.
MUN YI GWAJIN ‘SERVER’ A 2018, AMMA BA A YI AIKI DA ITA BA – Sayobi
Domin Kwamishinan Zabe na Kasa, Solomon Soyebi yace INEC ta yi amfani da ‘server’, amma a matsayin gwaji ba wai tattara sakamakon zabukan 2018 da aka maimaita. Amma ba tattara zabe 2019 aka yi a cikin ta ba.