Ma’aikatar kiwon lafiya ta karyata bullowar cutar Ebola a Najeriya

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta karyata rade radin da wasu kafafen sada zumunta na yanar gizo ke yadawa cewa wai cutar Ebola ya bullo a kasar nan.

Ma’aikatar ta ce wannan batu karya ne.

A bayanan da sakataren ma’aikatar Abdulaziz Abdullahi ya yi yace bai kamata mutane na sauraron batutuwan da babu tabbacin gaskiya a cikinsu ba.

Abdullahi ya yi kira ga mutanen Najeriya da su nisanta kansu daga yada batuttuwan da ba haka suke ba cewa yin haka na iya tada hankulan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

SAKON BULLOWAR EBOLA

Wasu mutane a kafafen sada zumunta na yanar gizo sun yada cewa cutar Ebola ya bullo a Najeriya.

Kafafen sun bayyana cewa an gano cutar ne a jikin wani mutum da ya shigo kasar ta iyakan jihar Legas.

A dalilin haka ake gargaddin duk asibitoci, ma’aikatan kiwon lafiya da mutane kan yin taka tsantsan da haka.

CUTAR EBOLA

Ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana cewa a kwayoyin cutar ‘Virus’ ne ke haddasa cutar.

Alamomin Kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, ciwon gabobin jiki, mura, rashin karfin jiki, rashin iya cin abinci, fitar da jini ta ido, hanci, baki, kunne da sauran su.

HANYOYIN GUJE WA KAMUWA DA CUTAR

1. A guji zama kusa da wanda ya kamu da cutar.

2. A guji cin naman biri ko kuma ‘ya’yan itattuwan da jemage ya ci ya bari.

3. A tabbatar an tsaftace muhalli tare da wanke hannu.

4. Gaggauta zuwa asibiti da zaran an kamu da zazzabi ko ciwon kai.

5. Idan ya kama za a ziyarci wanda ya kamu da cutar a yi amfani da safar hannu da rigunan kariya kafin a shiga wurin sa.

Share.

game da Author