Mona Mustapha Audu, wanda da ne ga Tsohon Gwamna Jihar Kogi, Abubakar Audu, ya shawarci masu rike da sarautun gargajiya su kaurace daga tsoma kan su cikin sha’anin siyasa.
Mustapha wanda ke takarar gwamnan Jihar Kogi a karkashin jam’iyyar APC, ya yi wannan kira ne ga sarakunan gargajiyar Kogi a ranar Alhamis a Abuja.
Ya yi bayanin ne a wurin wani taron manema labarai da ya gudanar, inda ya bayyana kudirorin sa da ya ke son cimmawa idan ya yi nasarar zama gwamnan jihar Kogi.
Da ya ke jawabi, Mustapha ya nanata cewa al’umma jihar Kogi ne za su ce ga wanda suke so zai zama gwamna, ta hanyar jefa masa kuri’a har ya yi nasara, ba wai sarakunan gargajiyar jihar ba.
Dan na tsohon gwamna marigayi Abubakar Audu, ya kara da cewa da a ce gwamna mai ci yanzu Yahaya Bello ya tabuka abin kirki a jihar Kogi, to da ba sai ya tsaya bata lokacin karakainar shiga Fadar Shugaban Kasa domin neman kamun-kafar sake tsayawa takatar a zabe mai zuwa ba.
Za a gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi da Bayelsa, a cikin watan Nuwamba mai zuwa.
Ya jajjada cewa ya shiga wannan takara ce domin kawai ya inganta ci gaban jihar Kogi da kuma al’ummar jihar baki daya.