Sanata Lawan ya yada kwallon mangwaro, ya fasa daukar mai caccakar Buhari aiki

0

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya soke daukar aiki da ya yi wa Festus Adedayo a matsayin Mashawarcin Musamman a Harkokin Yada Labarai.

Wannan sanarwa na ta fito ne daga wata sanarwa da Mataimakin Kakakin Yada Labarai na Lawan, Mohammed Isa ya sa wa hannu.

Duk da cewa dai ba a bayyana dalilin soke daukar ta sa da aka yi ba, duk da haka Sanata Lawan ya yi masa fatan alheri.

Sanata Ahmed Lawan ya nada Adedayo shekaranjiya Talata, sai dai kuma wannan mukami da aka ba shi ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan, musamman a cikin magoya bayan jam’iyyar APC da kuma ‘yan jarida.

Sun suna mamakin yadda aka bayar da mukamin ga Adedayo, wanda a tsawon shekara da shekaru ya maida hankali wajen ragargazar Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamnatin sa da kuma jam’iyyar APC.

A yau Premium Times Hausa ta bayar da labarin yadda aka rika ce-ce-ku-ce kan nada gogarman caccakar Buhari da Sanata Lawan ya yi a matsayin kakakin sa.

Nadin da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya yi wa wani fitacce kuma gogarman caccakar Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin kakakin yada labaran sa, ya haifar da surutai a fadin kasar nan.

Lawan ya nada Festus Adedayo Mashawarci Na Musamman a Harkokin Yada Labarai.

Adedayo ya taba zama mashawarcin tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi da Chimaroke Nnamani, tsohon gwamnan Enugu, duk a fannin yada labarai.

Sai dai kuma dimbin magoya bayan jam’iyyar APC, musamman a jaridu da sauran kafofi na soshiyal midiya, ba su ji dadin wannan nadi da aka yi wa Adedeyo ba.

Kafin nadin sa, Adedayo ya shahara kwarai wajen caccakar Buhari da manufofin gwamnatin sa da kuma APC ita kan ta.

Adedayo marubuci ne a shafukan jaridu da dama, ciki kuwa har da PREMIUM TIMES, inda ya ke ragargazar Buhari da gwamnatin sa.

Suka mai zafin da yak an yi wa gwamnatin APC, ta na jin ciwon sukar a tsikar jikin ta.

Wasu da dama ma ganin ma caccakar da kan yi wa Buhari, ta wuce suka har ta kai ga kiyayya da kabilanci.

Ko a kwanan nan sai da ya ragargaji Buhari dangane da wani yunkuri da gwamnatin tarayya ta yi domin bude gidan radiyo mai magana da harshen Fulatanci.

“Ina ji a jiki na cewa kafin Buhari ya kammala zangon sa na biyu ya sauka, sai Najeriya ta yi tarwatsewar da za ma daina batun wata Najeriya. Domin rikice-rikicen zamantakewa da na shugabancin da ke kunno kai cikin mu.” Inji Adedayo cikin wata ragargazar da ya yi wa Buhari kwanan nan.

Adedayo ya ragargaji shari’ar da aka yi wa tsigaggen Cif Jojin Najeriya, Walter Onnoghen.

“Irin yadda Buhari ke yi wa doka karan-tsaye, wata rana sai ya jefa Najeriya cikin ramin da kasar Cote d’Ivoire ta fada, shi kuma ya tsinci kan sa zaune a gaban Gbagbo tsohon shugaban Cote d’Ivoire.”

MUN YI MAMAKIN NADIN DA AKA YI WA ADEDAYO

Kungiyar Kara Muradin Shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar rubuta raddi da martani a kafafen yada labarai, mai suna Buhari Media Organization, ta bayyana mamakin yadda aka yi Sanata Ahmed Lawan ya nada Adedayo a matsayin Kakakin Yada Labaran sa.

BMO a ta bakin Shugaban Kungiyar, Niyi Akinsiju da Sakataren ta Cassidy Madueke, sun cika da mamakin yadda aka yi wannan kasassabar nadin Adedayo, ganin yadda tun bayan hawan Buhari shugabanci ya ke zagargazar sa da APC da kuma gwamnatin baki daya.

Daga nan sai kuma roki Ahmed Lawan wanda ya nada Adedayo da ya tsaya tsaf ya rika yi wa jam’iyya biyayya.

“Wannan abin mamaki da takaici ne ma, idan aka yi la’akari da yadda Adedayo bai taba gaba ganin wani abin alheri tattare da wannan gwamnatin ta APC ba, kuma bai taba yi mata fatan alheri ba, sai dai ragargazar ta tare da muzanta Shugaba Muhammadu Buhari.”

Daga nan sun ja hankalin Adedayo da kada ya sake ya jefa wannan gwamnati ko APC cikin ridu, kuma ya kasance ya na yi wa gwamnati da Buhari biyayya.

Share.

game da Author