Dan Najeriya ya ragargaza motoci a ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya

0

Wani hasalallen dan Najeriya ya afkawa ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Birtaniya, a Landon inda ya ragargaza motoci har guda bakwai.

Bisa ga bayanan da aka bayar bayan aukuwar abun, ance shi dai wannan dan Najeriya mai suna Jeffery Ewohime ya garzaya ofishin jakadancin ne domin ya karbi Fasfo dinsa da ya mika domin a sabonta masa.

Ance ko da yazo ofishin da misalin karfe 2 na rana sai ma’aikatan ofishin suka ce masa lokacin karbar Fasfo ya wuce sai kuma gobe.

Jeffery ya cije cewa lallai sai an bashi Fasfo din sa. Daga nan sai aka nemi ya mika shaidar da aka bashi lokacin da ya kawo Fasfo din ofishin sa.

Daga nan sai ya ce bashi dashi sannan ya fita a fusace.

Bayan dan wani lokaci sai ya dawo ya rika farfasa gilasan motocin da aka ajiye a gaban ofishin jakadancin ciki harda motar Jakadan Najeriya a kasar Birtaniya da wasu motoci biyu a gefe.

Akalla motoci 7 ya barnata.

‘Yan sandan Birtaniya sun cafke Jeffery Ewohime.

Kalli Bidiyo

Share.

game da Author