Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, ya jaddada cewa zai yi aiki tare da dukkan mambobin jam’iyyun adawa, musamman PDP a Majalisa.
Ya yi alkawarin raba mukamam shugabannin kwamiti har da PDP. Haka ya bayyana wa manema labarai jiya Litinin a Fadar Shugaban Kasa.
Wannan furuci da ya yi kuwa kamar bijirewa ce ga Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole.
Idan za a iya tunawa, shugaban na jam’iyyar APC ya fada kwanan baya cewa, jam’iyya mai mulki ba za ta raba mukamai a majalisa tare da PDP.
Sai dai kuma Gbajabiamila ya ce akwai kwamitoci hat 96 da ya ce dukkan mambobin majalisa da suka yi tazarce za a ba kowa shugabancin kwamiti daya. Su ma ‘yan adawa da sabbin shiga majalisa na PDP, duk wasu za su samu.
Ya ce a yanzu ana maganar ciyar da kasa gaba ne, ba wani abu ba.
Idan ba a manta ba, Oshiomhole ya ce su ma PDP a zamanin mulkin ta, ba a ba ‘yan adawa shugabancin kwamiti ko daya a majalisa ba.
Discussion about this post