Birkila ya falla wa Karuwarsa mari daya tal, nan take ta sheka lahira

0

A ranar Litini ne kotun dake Ilori jihar Kwara ta yanke wa wani birkila mai suna Sodiq Kazeem hukuncin dauri a kurkuku kan kashe wata karuwa a Otel.

Alkalin kotun Mary Bamidele ta bada umurnin a daure Kazeen a kurkukun Mandala dake Ilori har sai an kammala shari’ar

Za a ci gaba da shari’ar ranan 28 ga watan Yuni.

Lauyan da ta shigar da karar Rodah Kayode ta bayyana cewa Kazeem ya aikata wannan ta’asa ne ranar 30 ga watan Mayu.

Roda ta ce jami’an tsaro sun damke Kazeem bayan ya kashe karuwan mai suna Yemisi Adekoya a Otel din dake Coca- Cola dauke da fankan Otel din da ya sato.

“Bincike ya nuna cewa fada ne ya kaure tsakanin Kazeem da Yemisi kan rashin biyan ta kudinta bayan sun gama holewa.

” Kazeem yace sun yi da karuwan cewa zai biya ta Naira 2,500 sai aka samu akasi bayan ya gama sai ya ce wai kudin dake aljihusa ba za su kai yadda suka yi da ita ba.

” Yemisi ta falla mada mari nan take ganin cewa kudinta bai cika shi kuma da fushi ya dibeshi sai ya juwa ya gaura mata mari. Haka ke da wuya ashe yazo akan gaba wato ajali, nan take ta yanke jiki ta fadi ta mutu.

Sai dai kuma shi Kazeem ya musanta haka a kotu.

Share.

game da Author