A fili ta ke cewa kowa ya sani a duniya babu kasa mai karfin arziki da karfin makamai kamar Amurka. Sai dai kuma tabbatattun bincike-bincike da nazari da tsinkaye na nuna cewa Amurka na shayin haye wa Iran kai-tsaye, domin ko da ba ta iya kayar da ita, to za ta guntule mata kafa daya ko kuma hannu daya.
Hausawa kuwa sun dade su na cewa ‘dan hakin da ka raina shi ke tsone maka idanu.’ Watakila ma har ya iya makantar da idanuwan biyu.
Tun bayan da aka daina yakin-cacar-baki, baya ga kasar Koriya ta Arewa, babu wata kasa da ke fitowa gaba gadi ta na kalubalantar Amurka kai-tsaye kamar Iran.
A duk lokacin da Tehran ta samu dama, ba ta dage kafa ko sassautawa wajen caccakar Amurka musamman a duk inda ta ga Amurka din na wuce gona da iri wajen yin kaka-gida ko kane-kane a harkar tattalin arziki, siyasa, diflomasiyya, kisisisina, tuggu ko diflomasiyyar-kutunguiwa da algungumancin manyan kasashen duniya da Amurka ta sama yin katsalandan.
Tattalin kayan yakin da Amurka ke yi ta na girkewa a yankuna da kasashen da ke kusanci da Iran, musamman a cikin teku, ya na zama bazarana ga Iran.
Cikin shekarun nan, abin da Amurka ta kashe wajen makamai ya nunka tattalin arzikin Iran gaba daya.
A na ta bangaren, ita kuma Iran ta maida hankali wajen kara karfin makaman ta masu linzami wajen kara masu dogon zango da kara nauyin lodin bama-baman da za su rika dauka. Tare kuma da kara gyara musu saiti ta hanyar amfani da na’urorin zamani, yadda ko an harba ba su rika yin kuskure ba.
Hukumomin Tsaron Iran sun gamsu da kera makami mai linzami na zamani, wanda ya fi kowane mummunar barna. Suna kiran sa Shahab, wanda samfuri ne aka dauko daga Koriya ta Arewa.
YAKI SAI DA MAKAMI
Tabbas Amurka na tsoron mugan makaman Iran masu linzami samfuran SejjiI-1 da SejjiI-2. Iran ta taba gwada na farkon tun cikin 2008.
Ko a cikin 2009 a watan Nuwamba, sai da Sakataren Tsaron Amurka na lokacin, Robert Gates ya tabbatar da cewa makamin Iran samfurin SejjiI zai iya cin nisan kilomita 2,500 idan suka harba shi. Kuma zai isa cikin dan kankanin lokaci.
Shi ma Ministan Tsaron Iran, Mustafa Mohammed ya tabbatar da cewa SejjiI guda daya rak na iya daukar bam mai nauyin kilogram 750 ya je har cikin kasar Isra’ila ko wasu kasashen Turai ya jefa ya dawo.
Tsoron da Amurka da Turai da Isra’ila ke yi shi ne, kada wata rana Iran ta loda wa irin wannan makami mai linzami da bama-bamai na nukiliya ta cilla su Isra’ila ko wasu kasashen Turai.
Fitattun masana makamai na zamani na duniya sun tabbatar da cewa Iran ta gwada makamin SejjiI-2 cikin 2009. Kuma za a iya loda masa bama-bamai masu nauyin kilogram 650.
Sauye-sauyen karin inganci da suka yi wa wadannan tulin makamai a baya-bayan nan, an yi ittifakin cewa an yi musu garambawul ta yadda duk wanda aka harba, sai ya dangana da inda aka auna shi, ba tare da kuskure ba.
Sannan kuma kowane zai iya kai nisan zangon kilomita 2510, a cikin kankanin lokaci.
GHADIR, HATSABIBAN JIRAGEN KARKASHIN RUWA NA IRAN
Babban tsoron da manyan kasashen duniya ke wa Iran, musamman Amurka, shi ne yadda ta mallaki wasu hatsabiban kananan jiragen karkashin ruwa (submarines).
Ana kallo cewa wadannan barazana ce babba ga kasuwar hada-hadar danyen mai ta duniya. Domin kashi 20 bisa 100 na danyen mai da ake jigila da safara a duniya, sai ya bi ta Mashigar Ruwa ta Hurmuz, wato ‘Strait of Hormuz’.
Ana ganin idan daji ya yi dameji, to babu mai iya hana Iran ragargaje duk wani jirgin ruwan da ya bi ta wannan zirin hanyar ruwan teku zai gilma zuwa Turai.
Shi ya sa ma aka kiyasta cewa Amurka ta kashe sama da dala tiriliyan 8 daga 1976 zuwa yau, wajen kare wannan yankin ruwa na ‘Strait of Hormuz’, wato Mashigar Ruwa ta Hurmuz.
Cibiyar Nazarin Yaki ta Duniya (ISW) ta tabbatar da cewa Iran za ta iya aika kananan jiragen ta na yakin karkashin ruwa, dauke da muggan makamai su rika yin kwanton-bauta a kan duk wani babban jirgin da zai iya bi ta Tekun Arebiya, ta lalata shi.
Abin tsoron shi ne Iran ta mallaki irin wadannan kananan jiragen karkashin ruwa masu yawan gaske, kuma kowane ya na da nauyin tan 150. Sunan su Khadir ko Qadir, wadanda sun a da kamanceceniyar samfur da na Koriya ta Arewa masu suna Yugo da Sango.
Ko a cikin 2013, sai da Chris Harmer na cibiyar ISW ya ce wadannan jiragen karkashin ruwa na Iran abin tsoro ne matuka. Kanana ne, amma za su iya tarwatsa duk girman jirgin ruwa ko jirgin yaki na ruwa idan suka yi kwanton bauna a karkashin ruwa
YAKIN ’YAR-ROTOTUWA (drone)
Irin yadda dakarun kasar Iran suka harbo jirgin leken-asiri na kasar Amurka, ya tabbatar da cewa Iran ba kasar da Amurka za ta iya yi wa yadda ta ga dama ba ce. Kuma ta nuna wa Amurka cewa duk mai tsoron aradu, to shi ta ke fada wa.
Iran ta harbor jirgin nan na daukar bayanai mai sarrafa kan sa da kan sa, da aka fi sani da ‘drone’, wato ’yar-rototuwa. Ta kifo jirgin ne bayn ta leko shi ya na yi wa Amurka leken asiri a cikin kasar Iran.
Sai dai jirgin na ‘drone’ din na Amurka, ya sha bamban da duk wani jirgin rotutuwa na duniya, wajen girma da kuma tsada. An tabbatar da cewa Amurka ta kashe dala milyan 180 wajen kera shi. Kuma dauke ya ke da tulin bayanai na leke asiri kafin Iran ta kifar da shi.
MAKAMIN KHALIJ-E FARS (DILLALAN MUTUWA)
Iran ta tanadi tulin wasu kananan makaman linzami da ake harba wa a kan jiragen ruwa, wadanda ta rada wa suna ‘dillalan mutuwa’, kamar yadda ake yi musu kirari. Amma sunayen su a rubuce su ne ‘Khalij-e Fars (ASBM). Duk gudun jirgin ruwa, Iran na iya yin amfani da wadannan makamai ta kifar da su. Su na cin zangon kilomita ‘300 cikin kiftawa da bisimillah’.
Sannan kuma su na daukar bama-bamai masu nauyin kilogram 650. Sojojin ruwan Iran ne ke amfani da su. Kuma da na’ura suke aiki. Shi ya sa duk inda aka cilla su, to sai sun dangana.
Sannan kuma ana tsoron Iran za ta iya amfani da karfin da ta ke da shi a fadin duniya wajen masu goyon bayan ta, su rika kai wa Amurka da kasashen Turai hare-hare a wau kasashe. Musamman ana gudun Hezbollah da ke Lebanon, kan iyaka da Isra’ila.