Jami’in hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Gombe Danjuma Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ta raba maganin ‘Mectizan’ kyauta a kananan hukumomi 10 a jihar.
Mohammed yace gwamnati ta yi haka ne domin dakile yaduwar cutar kurkunu dake kawo makanta wato ‘River Blindness’da ta bullo a jihar.
“Tun a shekarar 2018 ne muka fara rabon wannan magani kuma ma’aikatan mu na bi lunguna-lunguna a wadannan kananan hukumomin domin dakile yaduwar cutar.
Akan kamu da cutar kurkunun dake sa makanta idan kudan da ke dauke da tsutsa a jikin shi da ake kira ‘Blackfly’ ya ciji mutu inda a dalilin cizon tsutsa ke shiga jikin mutum.
Wurin da kudan ya cija kan zama maruru saboda tsutsan da ya shiga jikin mutum ya ci gaba da girma.
Rashin cire wannan tsutsa kan sa ya shiga idon mutum wanda yake iya sa makanta ko kuma ya shanye kafar mutum.
Bayanai sun nuna cewa mazauna karkara musamman wadanda ke zama a kusa da rafi sun fi kamuwa da wannan cuta.
Bayan haka Mohammed ya ce maganin ‘Mectizan’ da suka raba a wadannan kananan hukumomin na kuma maganin cutar dundumi ganin cewa cutar na daga cikin cututtukan ya adaban mutanen wurin.
Ya ce za su ci gaba da raba wannan magani a kananan hukumomin domin samun nasarar kawar da wadannan cututtuka nan da 2020 da kuma wayar da kan mutane game da mahimmancin tsaftace muhalin su da ruwan da suke amfani dashi.