INEC ta fi sauran hukumomin kasar nan kara samun inganci –Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ta fi sauran hukumomin kasar nan saurin samun karin ingancin gudanar da ayyukan ta.

Yakubu ya yi wannan bayani ne cikin wannan makon, a wurin taron Sharhi da Nazarin Yadda aka gudanar da zaben 2019, a otel din Sheraton, Abuja.

Daya daga cikin Kwamishinonin Zabe na Kasa mai suna Mustapha Lecky ne ya wakilce shi a wurin taron.

Cikin wadanda suka halarta har da wakilatan kungiyar ECES ta Tarayyar Turai, IFES da Sakataren INEC, Daraktocin INEC da kuma jami’an yada labarai na hukumar.

Yakubu ya kara da cewa, idan aka yi la’akari da fadin kasar nan, da yawan al’umma da kuma yanayin zabukan da suka gabata a baya daga 1999, za a ga cewa wannan na baya-bayan nan, wato 2019, ya sha bamban sosai, kuma ya na da inganci fiye da kima.

“Saboda mu na da ofis a kowace karamar hukumar da ke fadin kasar nan. Sannan kuma dukkan ma’aikatan su na aiki tukuru kamar sauran yadda ma’aikatan kananan hukumomi ke aiki.”

“Duk da INEC na da dalilin da zai sa ta rika yin tinkahon nasarorin da ta samu, wannan ba zai sa ta tsaya a nan ba. Za ta kara neman ilmi tare da sanin yadda za ta kara inganta ayyukan ta fiye da yanzu.”

Daga nan ya ce wannan ne ma dalilin da ya sa ake shirya irin wannan taron, domin a ji yadda kowa zai yi bayanin irin abubuwan da aka ci karo da su a lokutan gudanar da ayyuka da sha’anin tafiyar da zabukan da suka gabata.

Sai ya yi kira ga wadanda suka halarci taro kowa ya fito ya bayyana abin da ya fuskanta ko ya ci karo da shi, domin hakan inji shi, zai taimaka wa INEC wajen kokarin ta na inganta zabukan da ke tafi a gaba.

Shugabar Kungiyar ECES, mai suna Maria Teresa, ta ce ECES a shirye ta ke ta yi aiki kafada da kafada da INEC, domin inganta zabe a Najeriya.

Ta ce irin wannan nazarin abin da ya biyo baya ya na da kyau, domin ta haka ne za a iya inganta abin da zai zo nan gaba.

Share.

game da Author