Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku jama’ah! Kamar yadda kuka samu labari, umurni yazo daga Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, na dakatar da Hawan Nasarawa na wannan Sallah karama ta 1440 bayan hijirah. Kuma Alhamdulillahi, bayan samun wannan umurni daga Gwamnati, sai Masarautar Kano ta fitar da sanarwar janye hawan, domin bin umurnin Gwamnati da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Sanadiyyar haka, Masarautar ta soke hatta Hawan Dorayi, domin samun rahoton sirri cewa, an samu labarin shirya wasu ‘yan ta’adda, bata gari, domin su tada hankali, su tada fitina a wurin hawan. Kasancewar Masarautar Kano mai kishin talakawan ta ce, mai nuna kauna da soyayya a gare su, shi yasa ta janye hawan dorayin, don kada a zubar da jinin bayin Allah da basu-ji-ba-basu-gani-ba!
Kuma sannan Masarautar ta Kano ta bada sanarwar cewa, maimakon hawan na dorayin da ya fado ranar Juma’ah, 7 ga wata (wato gobe kenan), ana gayyatar dukkan limamai da malamai da dukkanin jama’ah, wurin yin addu’a ga marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, da ya cika shekaru biyar da rasuwa. Da kuma yin addu’a ga Sarkin Kano na yanzu, Malam Muhammadu Sanusi II, da ya cika shekaru biyar a bisa gadon sarautar Kano. Tare kuma da yin addu’a ta Allah ya zaunar da Jahar Kano, da arewa, da Najeriya baki daya lafiya. Kuma za’ayi wannan addu’a ne a babban Masallacin Juma’ah na cikin birni, da karfe takwas daidai na safe (8:00 am), idan mai duka ya kai mu.
Don haka muna kira ga masu sha’awar ganin anyi bikin hawan Sallah a wannan Sallah da suyi hakuri, su dan saurara. Mun san da cewa wannan hanawar ba zai yi maku dadi ba. Amma dai don Allah abi umurnin masarauta, a zauna lafiya. Duk wani masoyin Sarki muna kira kar wanda yayi hayaniya da kowa, ko ya tada hankali. Dama mu an san mu, mu ba masu son tashin hankali bane. Mu mutane ne masu kaunar a zauna lafiya. Saboda haka don Allah abi doka da oda. Kamar yadda kuka sani, magana tana kotu, idan Allah yasa kotu ta kammala aikin ta, sai a harbi tsuntsu biyu da dutse daya. Ayi kara’in Hawan Sallah, sannan ayi murnar kurewar ramin karya da zalunci. Ai kamar yaune ga mai yawancin rai In Allah yaso.
Muna kira ga dukkan ‘yan uwa, Masoyan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, da aci gaba da yiwa Sarki Addu’a, Allah ya cigaba da bashi nasara akan dukkanin makiyan sa da magautan sa, amin.
Kuma muci gaba da rokon Allah ya bawa Mai Martaba Sarki hakuri, juriya da jajircewa da ikon cinye wannan jarabawa da yake fuskanta, don Alfarmar Shugaban mu, Annabi Muhammadu (SAW).
Kar muyi zagi, kar muyi hayaniya, kar muyi ashar, muyi ta hakuri. Daga karshe, mun san cewa Allah yayi alkawarin taimakon wadanda ake zalunta, kuma muna da yakinin zai taimake mu.
Don haka duk wani mai mulki ya sani cewa, duk karfin mulkin sa bai kai karfin Allah ba, don haka muna kai karar sa wurin Allah!
Duk wani mai mulki ya sani, duk zaluncin sa bai kai FIR’AUNA ba, amma yau ina yake?
Duk wani mai mulki ya sani, komai izzar sa da jabberancin sa da mutakabbirancin sa bai kai NAMARUDU ba, wanda karamar halitta daga cikin halittun Allah, SAURO, Allah ya aiko ya hallakar da shi.
Sannan bayan kotun cikin duniya da muka shigar da kara, wadda muke da yakinin da yardar Allah za’ayi muna adalci, muna masu kai karar duk wani mai hannu a cikin wannan al’amari a kotun Allah, bisa duk wani yunkurin wulakanci da cin mutunci da ko yaushe suke nufin Sarkin Kano da shi. Allah ya kaskanta duk wani mai hannu a cikin wannan al’amari, tamkar yadda ya kaskanta Abu Jahal, don alfarmar Annabi Muhammadu (SAW).
Muna kai karar ku wurin Allah, Allah ya isa bisa zaluncin ku na jiya, da na yau da kuma na gobe. Da karfin ikon Allah, sai Allah ya nuna maku isar sa, da buwayar sa, domin ku zama darasi da aya ga na bayan ku.
Ya Allah, muna rokon ka, muna kai kukan mu wurin ka, muna kai kara a gare ka ya Allah, duk wanda yake ganin abinda Gwamna Ganduje yake yi daidai ne, ka hada da shi cikin masifar da zaka dandanawa Ganduje tun a nan duniya, don alfarmar sunayen ka YA QAHHARU, YA JABBARU, YA MUZILLU, YA MUHLIKU, YA MUMITU, YA QABIDU!
Sannan ya ku ‘yan uwa! Ku sani, Addinin Musulunci Addinin Allah ne da ya shimfida hanyoyin zaman lafiya da jin dadin rayuwa. Kuma daga cikin manya-manyan dokokin ubangiji shine, ya wajabta yin adalci kuma ya haramta zalunci.
Wadannan dokokin Allah ya dora su har ga kansa. Don haka, Allah Tabaraka Wa Ta’ala ba ya zalunci kuma baya bari a zalunci bayin sa, kamar yadda ya fada a cikin hadisul-kudusi.
Sannan a cikin dukkanin Addinan da Allah ya saukar, ba Addinin da bai haramta zalunci ba, ga shi ko dan Adam an halicce shi da son yin zalunci da cuta kamar yadda Allah ya fada.
Imam Al-Hafiz Ibnu Kayyim al-Jauziyyah yana cewa:
“Asalin kowane alheri abu biyu ne: Ilmi da adalci. Haka kuma asalin kowane sharri daga jahilci ne da zalunci. Don haka Idan Allah yana son alheri ga mutum sai ya sanar da shi abinda ke amfanin sa, sai ya kawar da jahilci, sannan ya ba shi ikon amfani da shi sai ya gusar da zalunci.” [Duba littafin Igathatul Lahfan, 2/136-137]
Ya ku jama’ah! Hadarin zalunci yasa Manzon Allah (SAW) ya shelanta haramcin sa a taro mafi girma kuma mafi daraja da Musulmi suka taba yi a zamanin sa.
Hadarin zalunci yana kara hauhawa idan ya kasance ya auka ma jama’a masu yawa, ko wadanda aka sani ko wadanda ba’a sani ba.
Wannan shi yasa Manzon Allah (SAW) ya tsananta maganar cin dukiyar ganima kafin a raba ta kuma yace, duk wanda ya ci ta to ya ciwa kansa wuta.
Kuma da aka kashe wani yaron sa da ake ce ma Mid’am, Sahabbai suka ce, muna yi masa murnar shiga Aljannah, sai Manzon Allah (SAW) yace, sam ba haka bane, na rantse da Allah yana can yana ci da wuta a kan bargon da ya dauka daga cikin ganimar Khaibar. Da jin haka sai wani Sahabi yayi sauri ya dawo da saitin takalma guda daya da ya dauka. Sai Manzon Allah (SAW) yace, ka kuru, domin da sun zame ma ka takalma biyu na wuta.
Sannan ya ku ‘yan uwa ku sani, shi zalunci ba ya da kadan. Manzon Allah (SAW) yace:
“Duk wanda yaci zalun wani mutum da karfi, Allah zai haramta masa shiga Aljannah, sannan ya wajabta masa shiga wuta. Sai wani yace, ya Manzon Allah, ko da abin kadan ne? Sai Annabi (SAW) yace, ”Ko da karan aswaki ne.” [Muslim ya ruwaito shi]
Sannan daga cikin manyan bala’oin da zalunci yake haifarwa akwai:
1. Hana zaman lafiya da ci gaba.
2. Haduwa da hukuncin Allah da azabar sa.
Hadisi ya bayyana cewa, Allah Ta’ala ya azabtar da wata mata a kan kyanwa. To, ina ga bawan Allah mumini, ina kuma ga al’ummah mai dinbin yawa wadanda kila ba ka san iyakar su ba!!
3. Allah ba ya son azzalumai.
4. Zalunci yana haifar da duhu ga mai yin sa ranar alkiyama, ranar da kowa ke bukatar haske don tsallake siradi. Kamar yadda hadisi ya nuna.
5. Zalunci yana janyo halaka ga al’ummah.
6. A kullum wanda ke zalunci ba ya rabuwa da Allah ya isa daga jama’ah.
Wannan kuwa yana da matukar hadari.
Manzon Allah (SAW) yace wa Mu’az Dan Jabal (RA):
“Ka kiyayi Allah ya isar wanda aka zalunta, don ba ta da shamaki tsakanin ta da Allah.”
Haka kuma Abu Hurairah (RA) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW) cewa:
“Addu’ar mutum uku Allah na karbar su: Wanda aka zalunta da Matafiyi da Mahaifi.”
Kana can kana ta sharar bacci, kana ta sakin minshari, hankalin ka a kwance, ba ka tunanin kome, shi kuma wannan bawan Allah yana can yana dako, sai dare ya kai tsakiya ko ya kusa karewa, a cikin duhu zai tashi, cikin natsuwa yayi alwala ya kabbarta Sallah…idan ya kai goshin sa kasa sai ya tartsa wa Allah kuka, a daidai lokacin da Allah ke shelar: Ina mai kirana in karba ma sa? Ina mai neman agaji na in agaza masa? Ana haka ne zai kai karar ka ga buwayayyen Sarki. Don haka ne sai ka ga kwatsam, al’amarin mutum ya dagule, basirar sa ta toshe, dabarar sa ta kare, jarin sa ya kare, ikon sa ya gushe, lafiya ta karanta a gare shi, jin dadi ya kau, jama’a sun watse, an bar shi da tarin zunubi, da yawan bakin ciki da karancin jin dadi…Wannan duk karamin aikin Allah ya isa kenan. Wannan shine abin da Sarki Khalid al-Barmaki ya fada wa dansa a lokacin da aka tsare su a kurkuku, yaron yace, Baba! dubi halin da muka fito kuma dubi yanayin da muka samu kan mu. Sai Sarki Khalid yace masa, Allah dai ya kiyaye. Watakila wani ne yayi muna Allah ya isa muna can muna ta bacci.
Wani fursuna yayi wa Sarki Khalid Bin Abdullah al-Kasari wa’azi mai kama da haka a lokacin yana gwamnan Khurasan sai ya kai ziyara gidan kaso yana raba ma fursunoni kyauta. Da ya kawo ga wannan bawan Allah sai yace masa: In don ka tausaya kake bayar wa to, tausaya ma kanka daga wanda ka zalunta. Yi hattara da wanda bai da kowa sai Allah, bai da wani makami sai addu’a. Ka sani kofofin sama gaba daya budewa suke yi idan ance, Allah ya isa.
7. Allah ba ya shiryar da azzalumi.
8. Azzalumi zai gamu da sakamakon zaluncin sa tun a nan duniya.
9. A ranar Al-kiyama azzalumi zai zama abin tausayi.
A ranan ne azzalumi zai nemi ya ba da fansa da duk abinda ya mallaka, ciki har da dan jarin sa na duniya, kai da ma duk abinda ake so in zai samu. Amma ina!
10. Ba yadda za’a yi a shiga Aljannah tare da digon zalunci, domin kuwa ko bayan tsallaka siradi ba’a shiga Aljannah har sai an kawar da zalunci kowane iri, an kwatar wa kowane mai alhaki hakkin sa. Abu Sa’id al-Khudri (RA) ya karbo daga Manzon Allah (SAW) cewa:
”Idan muminai suka tsallaka siradi za a tsayar da su a kan wata gada da ke tsakanin Aljannah da wuta, sai a caje su da wasu laifukka na zalunci da suka gudana a tsakanin su. Sai an gama tsarkake su tsab sannan ayi masu izinin shiga Aljannah.”
Sannan Manzon Allah (SAW) yayi rantsuwa cewa, idan suka shiga Aljannah kowa zai gane gidan sa fiye da yadda yake gane gidan sa na duniya. [Sahihul Bukhari]
Sannan babu shakka shugaba in ya zamo azzalumi to hadarin sa yafi girma, wannan shi yasa za’a zo da kowane shugaba koda na mutum goma ne a daure ranar Al-kiyama sai dai idan yayi adalci adalcin nasa ya warware shi kamar yadda ya tabbata a cikin hadisi. [Duba Sahihul Jami’, 5571 da Silsilah as-Sahiha 344]
Ya ku bayin Allah! Wanda ya fada a cikin zalunci alhakin sa a kan mu shine mu taimake shi. Ta yaya zamu taimake shi? wannan shine abinda Sahabbai suka tambayi Manzon Allah (SAW) a lokacin da yace:
”Ka taimaki dan uwanka ko shi ke zalunci ko shi aka zalunta.”
Amsar da Manzon Allah (SAW) ya basu ita ce, taimakon azzalumi shine a kange shi a hana masa yin zalunci. Allah Ta’ala na iya yiwa azzalumi daurin talala amma ba zai taba kyale shi ba. Sau da yawa kuma Allah yake sallada wani azzalumi don ya darkake wani. Kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya fada.
Ya ku jama’ah! A nan duniya azzalumi na iya samun girma da kima ko don kwadayin abin hannun sa ko don gudun sharrin sa, amma a ranar alkiyama babu wulakantacce marar daraja da kima irin sa. Sai dai yana da kyau mu sani cewa, ko meye girman zalunci yana da tuba kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya fada.
Don haka, ya kai azzalumi! Allah ya bude kofa gare ka, ya kai dan Adam mai yawan zalunci. Ka tuna duk irin nau’in jama’ar da ka zalunta. Sannan ka bi hanyar sasantawa da su tun ba’a tafi lahira ba suka nemi ladar ka a lokacin da kafi kome bukatuwa zuwa gare ta, kuma a rannan kana ji kana gani za’a ba su ladar azumin ka da umarar ka da sauran ibadar ka.
Ya ku jama’ah! Ku sani, wannan shine zalunci. Don haka wallahi, duk matsalolin da kuke ganin muna samun kawunan mu a ciki, suna faruwa ne saboda zaluncin da azzalumai suke tafkawa. Allah ya shiryar da mu, amin.
Dan uwan ku,
Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.