Hukumar NBC ta dakatar da AIT da tashar radiyon Ray Power

0

Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talbijin ta Kasa, NBC, ta janye lasisin yada labarai na Kamfanin Daar Communications Ltd.

Kamfanin Daar Communications, mallakar Raymond Dokpesi, su ke da gidan talbijin na AIT da kuma Gidan Radiyon Ray Power a fadin kasar nan.

Babban Daraktan NBC, Modibbo Kawu ne ya sanar da wannan dakatarwa a yau Alhamis a Abuja, a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa NBC ta zargi AIT da laifin karya dokar yada labarai ta gidan talbijin a cikin wasu shirye-shiryen ta.

Amma dai Shugaban Daar Communications, Dokpesi, ya zargi NBC da laifin yi wa ‘yan fadar albarkacin baki takunkumi.

Jama’a da daman a sukar wannan kakkausan mataki da NBC ta dauka, wanda ake ganin cewa ta dauke shi ne saboda an soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Share.

game da Author