SHUGABANCIN MAJALISA: Dalilin da ya sa na janye wa Lawan – Goje

0

Sanata Danjuma Goje ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya janye wa sanata Ahmad Lawan daga takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa shine domin saka baki da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Idan ba a manta ba tunda sanyin safiyar Alhamis ne gwaman jihar Kaduna ya jagoranci Sanata Ahmad Lawan da tsohon gwamnan jihar Gombe, Goje zuwa fadar shugaban kasa domin yin ganawar sirri da shugaba Buhari.

Bayan kammala ganawar, sai dukkansu suka zanta da manema labarai. Goje yace sun ziyarci fadan shugaban kasa ne domin sasanta tsakaninsu musamman dan takarar kujerar wato sanata Ahmad Lawan.

Dama can su uku ne ‘ya’yan jam’iyyar APC suke neman darewa kujerar.

Akwai shi Ahmad Lawan din, sanata Danjuma Goje da sanata Ali Ndume.

Goje da shima yana daga cikin wadanda ke kan gaba wajen neman zama shugaban majalisar dattawan ya bayyana wa manema labarai cewa dukkan su ya’yan jam’iyya daya ne kuma burin su shine a samu hadin kai da nasara a majalisar ba kamar yadda aka rika samun baraka a baya ba.

” Na janye na hakura na bari wa Ahmad Lawal, ni yanzu na zama dattijo sai dai in bada shawara sannan kuma da tattaunawar da muka yi da shugaban kasa Buhari game da hakan duk ya dada sa na ji na janye daga takarar.

Shima gwamnan Kaduna da shine jagoran tafiyar ya jinjina wa Goje bisa wannan mataki da ya dauki da kuma kuma amsa kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi.

Share.

game da Author