Ban ce sojojin Najeriya sangartattu bane –Buratai

0

Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Tukur Buratai, ya musanta labarin ya aka rika watsawa tun cikin makon da ya gabata, inda aka ce ya ce a yanzu Boko Haram na kara kaimin kai hare-hare ne, saboda sojojin Najeriya a karkashin sa sun daina nuna kishin yakin kare martabar kasar su.

Laftanar Janar Buratai ya ce ko ta halin kaka dai an jirkita masa magana ta yadda aka isar da sakon sa a karkace, ba kamar yadda ya furta da bakin sa ba.

Ya ce wasu bangarori ne na kafafen yada labarai suka yi wa kalaman sa mummunar fahimta da nufin kitsa masa sharri kawai.

Buratai ya yi wannan raddi ne a wani taron manema labarai da ya gabatar a Maiduguri tare da Gwamnan Jihar Barno, Babagana Umara, a lokacin da ya kai wa gwamnan ziyara.

“Ban taba furta cewa sojoji sun sangarce ba su da kishin yakin kare martabar kasar su ba.” Inji Buratai.

“Kawai dai wasu sashe ne na kafafen yada labarai suka kantara min karya da kuma kuntuka min sharin fadin abin da ni ban fada ba, kuma babu inda na fada.

“Idan aka duba shafin intanet na sojoji, za a ga tantagaryar furucin da na yi, babu ragi kuma babu kari a ciki.”

“Wasu ‘yan jaridar ma har da yi min karin-gishiri, suka ce wai na ce sojoji matsorata ne. Wannan kwata-kwata ba gaskiya ba ne. Kuma abin takaici ne irin yadda wasu ‘yan jarida da gidajen jaridu ke wuce-gona-iri su na dagula gaskiya ta hanyar shafa mata bakin fenti.”

Sai dai kuma Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Talatar da ta gabata, ya ruwaito Buratai ya na cewa sojoji na nuna rashin nuna hobbasar kare kasar su. Wannan matsala ce ya ce abin takaici ne matuka, kuma ta janyo jan-kafa wajen yi wa kananan sojoji karin igiya.

A jawabin da Buratai ya yi jiya Litinin a Maiduguri, ya jaddada cewa:

“Akwai abokan gaba mabarnatan masu laifi a cikin al’umma, kuma su na karakainar su a ko’ina. Har sai an iya gane mugun iri daga cikin mutanen kirki ne za a iya magance su da kuma dakile su.” Inji Buratai.

“Amma matsawar ba a iya gano su ba, al’umma ba su iya nuna su ba, kuma suka ci gaba da gauraya a cikin jama’a, to za mu ci gaba da fuskantar barazana, sannan kowa ma zai ci gaba da shan wahala.

Share.

game da Author