Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya shata sabbin ajandojin inganta tattalin arzikin Najeriya na tsawon shekaru biyar da zai sake yi ya na shugabancin bankin.
Daga cikin ajandojin akwai mudadin samar wa kusan kashi 95 na duk wani dan Najeriya da ya cancanta samun tallafi na lamuni nan da shekarar 2024.
Akwai kuma gagarimin kokari da hobbasa da CBN zai yi domin kara lafta wa bankunan kasuwanci jarin jin saukin tafiyar da hada-hadar kudade.
Emefiele ya yi wannan jawabin jiya Litinin a lokacin da ya ke kaddamar da sabbin shirye-shiryen san a shekaru biyar masu zuwa.
Gwamnan na CBN, ya yi ikirarin da kan sa cewa har yanzu akwai wasu ajandoji da ba a samu damar cimma ba, bayan kuma tun cikin 2014 aka dauki alwashin za a cim masu kafin 2019.
Ya ce wadansu kalubale ne da aka rika cin karo da su suka haddasa haka. Sai dai kuma ya ce a wannan karo, ya na da tabbacin cewa CBN zai kai gacin da kowane dan Najeriya ke son ya ga bankin ya kai nan nan da shekaru biyar masu zuwa.
Daga nan sai ya fara warware zare da abawar nasarori da kalubalen da CBN ya samu cikin shekaru biyar da suka gabata.
Ya yi kuma nuni da cewa tare da yawan tuntuba da goyon bayan kwararru da hukumomin kula da hada-hadar kudade da masu ruwa da tsaki, CBN zai cimma wannan kudiri da ta dauka a yanzu.
Ya ce ya na daga cikin sabbin kudirorin CBN rage hauhawar tsadar farashi da rage rashin aikin yi da kuma zauna-gari-banza sosai da sosai.
Sannan kuma ya ce CBN zai kara wa bankunan kasuwanci kaimi da kwarin guiwar tallafawa wajen inganta ilmi, kara samar wa Najeriya kudade a asussun ajiyar kasashen ketare tare da fadada tattalin arziki musammam a bangaren noma da habbaka masana’antu.
A cewar sa, CBN zai iyakar kokarin sa wajen ya kara inganta darajar naira, tare da rike wa dalar Amurka da sauran manyan kudaden Turai linzamin da ba za su rika tashin-gwauron-zabo ba, su na barin naira a kasa ba.
Emefiele ya ce zai yi kokarin ganin an rage kudaden ruwan da bankuna ke dora wa masu karbar lamuni domin yin kasuwanci ko gina masana’antu.
Sannan kuma za a yi kokarin daidaita darajar kudi da ta abinci, ta yadda farashin abinci zai sauko daidai gwargwadon nauyin aljihun talaka.