ZABEN 2019: INEC ta kwace shaidar ‘yan takara 25 bisa umarnin kotu

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana kwace satifiket har 25 daga ‘yan takarar da baya aka bayyana sun yi nasara.

Ta ce umarnin koto ne INEC din ta bi, bayan wasu da suka kai kararraki a kotuna sun yi nasara.

Babban Jami’in INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka jiya Litinin a Enugu yayin da ya ke jawabi wajen taron da Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Kasa (NUJ) ta shirya

NUJ ta shirya taron ne domin tattauna rawar da INEC ta taka a zabukan 2019 da ta gudanar.

Okoye ya ce an kwace satifiket 20 na shaidar lashe zabe daga dan Jam’iyyar APC zuwa wani dan APC. Sai kuma 2 daga dan PDP zuwa wani dan PDP. Akwai cikon 3 daga APC da PDP zuwa wasu jam’iyyu.

Ya jinjina wa kafafen yada labarai bisa gagarimar rawar da suka taka kafin zabe, lokacin gudanar da zabe da kuma bayan kammala zabe.

Okoye ya ce kafafen yada labarai ne daukacin talakawa suka rika dogara da su, domin samun bayanan yadda zabuka ke gudana. Ita kan ta INEC ta rika yin amfani da su domin isar da sakonnin ta ga jama’a.

Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida na Kasa, Chris Isigozu, ya yaba wa INEC dangane da yadda ta rika shirin gudanar da zabe, yadda ta gudanar da zaben da kuma bayan zabe.

Shi ma Kwamishinan Zabe na Jihar Enugu, Mr. Onomamadu, ya yaba wa kafafen yada labarai, sannan ya ce sun zuba ido domin ji da ganin yadda ‘yan jaridu, jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai za su yi sharhi a kan yadda INEC ta gudanar da zabukan 2019, domin koyon darasin kara inganta matakan zabe a gaba.

Share.

game da Author