GARKUWA DA MUTANE: An damke wanda ya sace surikin gwamna Masari da wasu 70

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta bada sanarwar kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane da suka wuce 70.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Sanusi Buba ne ya bayyana haka, a yayin da ya ke wa manema labarai bayanin nasarar da aka samu, tun bayan kafa ‘Operation Puff Adder’ a Jihar Katsina.

Ya ce daga cikin wadanda aka kama har da wanda ake zargi da yin garkuwa da surikar Gwamna Aminu Masari, mai suna Hauwa Yusuf.

An dai yi garkuwa da Hauwa a ranar 9 Ga Maris, 2019 bayan an je har cikin gidan ta an sace ta a cikin Katsina.

Buba ya ce an samu bindigogi kirar AK 47 har guda 43 a hannun wadanda ake zargi. An kuma samu motoci biyar, babura 44, bindigogin gargajiya guda 19, albarusai 1,500 da wasu kananan makamai.

Ya ce dukkan su sun amsa laifin su, kuma su na yi wa jami’an tsaro karin haske.

Wadanda aka kama da laifin sace surikar Masari sun hada da Abdullahi Sani, Abubakar Dani, Rabe Hamza, Gide da kuma Abdulkarim Bishir.

Ya ce ba da dadewa ba za a gurfanar da su kotu bayan kammala binciken su.

Idan ba a manta ba, an sace surikar Gwamna Masari har tsawon makonni biyu, inda aka sako ta bayan an biya diyyar naira milyan 30.

Har yanzu kuma Magajin Garin Daura ya na hannun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sama da makonni biyu da suka gabata.

Share.

game da Author