SUNAYE: Mashahuran attajiran da suka mallaki kamfanin MTN

0

Ranar Alhamis ne Hukumar Cibiyar Hada-hadar Hannayen Jari ta Najeria, ta shigar da kamfanin sadarwar layin MTN a cikin masu hannayen jari na Kungiyar da ke kula da hada-hadar, wato NSE.

Wannan kuwa ya bai wa jama’a damar sani ko kuma gano ainihin wadanda suka mallaki wannan takafaren kamfani.

Yawancin mutane a Najeriya sun dauka cewa Gwamnatin Tarayya na da hannun jari a cikin kamfanin MTN, da aka rika zargin ta mallaka ta hannun Hukumar Zuba Jari ta Najeriya (NSIA).

Sai kuma bayan an shigar da MTN a cikin jerin kamfanonin da ke cin kasuwar hada-hadar hannayen jari, an gano cewa babu Najeriya a ciki.

PREMIUM TIMES ta gano cewa jarin NSIA ya yi karancin da ba zai iya shiga cikin wannan sahun ba.

Takardun bayanan da NSE ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa mutane ko kuma a ce kamfanoni 11 ne suka mallaki MTN.

Su 11 din sun mallake hannayen jari bilyan 20,354,513,050 na ilahirin kamfanin na MTN, wadanda aka kiyasta kudin su ko darajar su ta kai naira biliyan 407.1 ya zuwa ranar da suka nemi a saka MTN din cikin kasuwar hada-hadar hannayen jari, a ranar 15 Ga Mayu, 2019.

GA SUNAYEN WADANDA SUKA MALLAKI KAMFANIN MTN

1. MTN International (Mauritius) Limited, Naira biliyan N309,710,881.

2. Stanbic IBTC Asset Management Limited na da naira biliyan 39,765,381 0.0977.

3. Hermitage Overseas Corporation na Da naira biliyan 16,137,738 0. Victor Odili Nigeria.

4. Mobile Telephone Network N.I.C.B. na da naira biliyan 11,194,403 0.02

5. Government Employees Pension Fund na da naira biliyan 7,105,633,000.00

6. Celtelecom Investment Limited na da naira biliyan 6,669,482 0.0164, wanda Pascal Dozie Nigeria ke da shi.

7. One Africa Investment Limited na da naira biliyan 5,301,843 0.013. Sani Mohammed Bello ne mai kamfanin.

8. Universal Communications Ltd na da naira biliyan 4,010,528,000.00 Babatunde Folawiyo ne mai kamfanin.

9. N-Cell Limited na da naira biliyan 3,269,751,000.00. Gbenga Onyebode ne mai wannan kamfanin.

10. SASPV Limited na da naira biliyan 2,888,580,000.00. Ahmed Dasuki Nigeria Ltd ne mai kamfanin.

An kafa kamfanin MTN a ranar 6 Ga Nuwamba, 2000, amma bai fara aiki ba sai a cikin 2001. Tun daga ranar MTN ke ci gaba da hada-hadar sa a Najeriya yau tsawon shekaru 18 kenan.

A Najeriya MTN na da kwastomomin da ke amfani da layukan sa har mutane miliyan 67.

Kuma shi ne kamfanin wayar selula mafi yawan jama’a da kashi 39 bisa 100 na yawan ‘yan Najeriya masu wayar selula.

Share.

game da Author