KUDIN TAFIYA HAJJI: Yaushe za a daina hajijiya da aljifan talakawa?

0

Daga ranar Asabar da ta gabata zuwa yau, jihohin kasar nan suna ci gaba da bayyana farashin tikitin jirgi zuwa Saudi Arebiya, domin zuwa aikin Hajji na 2019.

Hakan ya biyo bayan bayyana farashin da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kusan yawancin jihohin Arewacin kasar nan duk sun yanka naira miliyan daya da rabi da doriyar dubbai a kai, a matsayin kudin da Bahaushe ya fi sani da suna kudin kujerar Hajji.

Jihar Kaduna ta yanka naira milyan 1.549,297 a matsayin kudin kujera.

Haka sauran jihohi har da Abuja, duk naira milyan daya da rabi da doriya suka yanka.

Maniyyatan Jihar Kaduna za a ba su dalar Amurka 800 a matsayin kudin guziri daga cikin kudin da suka biya.

Sai dai kuma wanda zai tashi daga Kaduna, matsawar ya taba zuwa aikin Hajji shekaru hudu da suka gabata, to zai ga an yi masa karin Riyal 2000 a matsayin kudin cajin da Saudiyya ke yi wa Mahajjata hidindimu.

Wato dai idan ka je a 2015, to yanzu idan z aka koma a 2019 sai ka yi karin ladar kudin yi maka hidima har naira 162,000.00 idan daga Kaduna ka tashi.

KUDIN GORO

Ba kamar shekarun baya ba da ake kebe kudin karamar kujera, matsakaiciya da kuma babbar kujera, a bana 2019 kudin goro kawai aka yi, kowace jihar. Sai fa bambancin wasu dubunnai da wasu jihohi suka kara, wadanda na wasu jihohin sun fi na wasu yawan doriyar da suka kara a saman naira milyan 1.5 din.

A duk wanda ya je aikin Hajji na 2018, to idan zai koma a 2019, zai ga an yi masa karin naira 33,000.00.

KOWA YA TUNA BARA

Hausawa na cewa, “kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba. yayin da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi suka fara yekuwar kowa ya gaggauta biyan kudin tafiya Hajjin 2019, jama’a da daman a ta kokawa kan irin yadda farashin ke hauhawa, maimakon a ce an samu sauki a wannan gwamnatin.

2014: Lokacin tafiya aikin Hajjin 2014, Shugaba Goodluck Jonathan ya amince da rage wa dala daraja zuwa naira 160, domin maniyyata su samu sauki.

Hakan ya sa an biya kudin karamar kujera naira 735,561, ita kuwa babbar kujera naira 813,561.

2015: wannan ce shekarar da Muhammadu Buhari yahau mulki, kuma daga nan aka fara samun tashin farashin kudin kujerar jirgi domin tashi zuwa aikin Hajji.

An biya karamar kujera naira 758,476, ita kuma ta tsakiya naira 798,476. Sai babbar kujera kuma naira 897,476.

Kujerun duk daya ne, sai dai kawai wurin bada kudin guzuri ga maniyyaci idan ya sauka Saudiyya ne ne ake bambancewa.

A 2014, an rika biyan dalar Amurka 750 a matsayin kudin guziri ga mai karamar kujera. Matsakaiciya kuma an biya shi dala 1000, shi kuma mai babbar kujera aka bas hi naira 1,500.

Amma kuma yanzu a cikin 2019, dala 800 ne za a bai wa maniyyaci a matsayin kudin guziri idan ya zauka kasar Saudiyya, duk kuwa da cewa cewa ya lale naira milyan 1.5 har ma da wasu doriyar dubbai a matsayin kudin tafiya aikin Hajji.

Shin ko talaka nan gaba zai iya zuwa aikin Hajji idan naira ba ta kara daraja ba? Sai yaushe za a samu canji ko sauki ko rangwamen da aka yi tunanin samu tun shekaru hudu da suka gabata?

Duk maniyyacin da za a damka wa kudin guziri dala 800, to fa ya kwana da shirin cewa ko kusa da naira 350 kudin ba su kai ba.

Gaskiya ana tafiya aikin Hajji. Amma fa ana hajijiya da aljifan talakawa a ‘yan shekarun nan.

Shi kuma attajiri, ai ko a jikin sa.

Share.

game da Author