Lokacin da turawan mulkin mallaka suka zo Nijeriya, sun samu daga kudancin Nijeriya har zuwa arewacin Nijeriya ana gudanar da mulki ne karkashin sarakunan gargajiya.
Toh suma turawan mulkin mallaka a Nijeriya, sai suka ci gaba da amfani da sarakunan gargajiya amma umurni daga gare su sarakunan suke karba. Suna amfanin da sarakunan gargajiyan su karbi kudin araji, idan ba ka da kudi su karbin abinda ka noma kokuma a wulakanta ka. Toh wadannan arajin da kayan gona da muke nomawa ne turawan mulkin mallaka na Ingila (England) suka gina kasar su da shi.
YADDA TURAWAN MULKIN MALLAKA SUKA RAGE DARAJAN SARAKUNAN GARGAJIYA A NIJERIYA
Turawan mulkin mallaka na kasar Ingila (England) su suka kwacewa sarakunan gargajiya marbansu, Ikon su, mulkin su, da darajan su. Suka damka su hanun yan siyasa. Lokacin da za su bar kasan nan, zasu ba Nijeriya yancin kai. Salon mulki irin na Firai Minista (Prime Minister) da kuma Dimokaradiyya ne ya rage darajan sarakunan gargajiya, domin sun koma karkashin yan siyasa. Tun daga nan darajan sarakunan gargajiya ya ragu.
Za kaga babban sarki mai daraja na daya (First Class Chief) yana karban umarni daga hanun shugaban karamar hukuma (Local Government Chairman). Sannan akayi doka wai gwamnan jihar shi yake da Ikon zaban sarkin, sannan duk kudaden su daga hanun shi gwamnan zai fito. Idan gwamna yaga dama zai sa sarki yau, kuma ya cire shi gobe. Toh kaga ai abu ya lalace, yan siyasa su ke da Ikon da sarakunan gargajiya sai abinda da suka ga dama zasu yi kenan.
SHAWARA GA SARAKUNAN GARGAJIYA
Sarakunan gargajiya shawara na gare ku shi ne, tunda Turawan Mulkin Mallaka sun kwace muku daraja sun makawa yan shiyasa, toh ku abinda za su yi shi ne, duk yadda za’ayi kada ku rabu da TALAKAWA, ku rike talakawan ku da kyau, ku gyautata musu. Wallahi idan kuna gyautatawa TALAKAWAN ku, toh duk dan siyasan da ya taba ku, TALAKAWA zasu taba shi, ai dimokaradiyya ake yi, da yawa ake gadara. Saboda haka martabar ku da aka kwace zata dawo ne idan kuna kyautata wa TALAKAWAN ku, idan aka taso muku, sai su tsare muku ranan zabe, su kayar da wanda ya taba ku. Idan kuma mulkin mallaka kuke yi wa talakawan ku, sai su bar ku da yan siyasan.
Allah ya ba mu zaman lafiya a kasar Nijeriya, ya bamu damina mai albarka. Amen.