An kiyasta cewa rikicin makiyaya da manoma tsakanin 2015 zuwa 2019, ya ci rayukan ‘yan Najeriya 7,000 a jihohin Benue da Nasarawa da yankin Tsakiyar Najeriya.
Hukumar Agajin Inganta Cigaban Al’umma ta USAID ce ta bayyana haka.
Wata kungiyar sa-kai ce wadda ba ta gwamnati ba mai suna Mercy Corps, ta gudanar da binciken kuma ta rubuta wannan rahoto.
Kungiyar ta ce makasudin wannan bincike shi ne domin a gano hanyoyin da za a bi a magance wadannan matsaloli na kashe-kashe tsakanin Fulani makiyaya da manoma da ke ta furuwa a fadin Kasar nan.
Cikin wadanda suka halarci taron gabatar da rahoton har da babban basaraken kasar Tivi, Tor Tiv Jamed Ayatse, daraktan kungiyar Mercy Corps, Darious Radcliffe, babban jami’in USAID, Beatrice da sauran shugabannin yankunan al’ummar cikin karkara.
Rahoton ya kara da cewa ayyukan da kungiyar Mercy Corps ke yi a yankunan ya rage tashe-tashen hankula da kashi 13 isa 100.
Daga cikin horos da Mercy Corps ke bai wa jama’a, ta ce an warware husuma mai tarin yawa, wadda hakan ya hana a kai ga daukar makamai ana kashe juna.
Ta sasanta rigingimu sama da 600 wadanda suka shafi kiwo da, cin iyakoki da kuma na burtalin hanyar shanu.
Ta sasanta rigingimu shiga gonaki da dabbobi ke yi, wuraren ban-ruwar dabbobi, cin amfanin gona, sare itatuwa da sauran su.
Madakin Lafiya a Jihar Nasarawa, Ishaku Dauda, ya ce USAID Mercy Corps ta kawo zaman lafiya a cikin yankunan al’ummar su.
Ya ce akwai ma lokacin da saboda kauce wa rikici, sai da kungiyar ta gina rijiyar burtsatse ga makiyaya da manoman yankin sa.
Daga nan ya gode wa kungiyar bisa kokarin da ta ke yi matuka.
Da yawan mazauna yankin sun bayyana cewa a da zaman doya da manja suke yi, amma sanadiyyar USAID Mercy Corps a yanzu ana zaman lumana da fahimtar juna.