ZARGIN JUYIN MULKI: Atiku ya nemi a damke Lai Mohammed

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta damke Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed.

Atiku ya ce Lai ya yi zargin cewa wasu na yunkurin shirya wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasan juyin mulki, amma ya kasa gabatar da hujjojin haka din.

Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, ya kuma kira da Ministan ya rubuta masa takardar neman afuwa bisa kage da sharrin da ya yi masa.

Ya ce yin hakan zai sa Lai ba za ya sake yin irin wannan kasassabar magana ba, wadda ke da barazana ga tsaron kasa.

“Ganin yadda jaridar PREMIUM TIMES ta gudanar da bincike kuma ta buga sahihin labara mai dauke da cewa babu wani yunkurin juyin mulki, don haka Atiku ya na neman a gaggauta damke MinistannYada Labarai, sannan kuma ya rubuta takardar neman afuwa ga Atiku din.”

Haka Kakakin Yada Labarai na Atiku, Paul Ibe ya fitar a cikin wata sanarwa jiya Alhamis.

Wannan kira da Atiku ya yi, ya zo ne bayan kwana biyu biyan PREMIUM TIMES ta gudanar da binciken kwakwaf a kan takardun da gwamnati da jami’an tsaro suka ce an fitar ana kiran a kifar da gwamnatin Buhari.

Sai dai kuma kwakwaran bincike ya tabbatar da cewa maganar duk shaci-fadi ce, babu kamshin gaskiya a ciki.

Su kan su bangarorin jami’an tsaro da ofisoshin diflomasiyya sunnkasa tabbatar da wannan zargi da Lai ya yi.

Wannan magana maras tushe balle makama ta sa Atiku da kungiyoyin kare dimokradiyya sun fara cewa jami’an tsaro na kokarin bin irin turbar da Sani Abacha ya yi, inda gwamnatin sa ta kitsa karyar cewa ana kokarin juyin mulki.

An ce Abacha ya yi amfani da wannan dama don kawai a garkame masu adawa da mulkin sa a cikin shekarun 1990.

Bayan da PREMIUM TIMES ta buga cewa batunn zargin juyin mulki duk tatsuniya ce ba gaskiya ba ce, Lai Mohammed ya sake fitowa ya ce gwamnatinn tarayya na da ‘cikakkar hujjar’ cewa akwai yunkurin masu adawa na neman yi wa gwamnati zagon kasa.

Sai dai kuma yayin da PREMIUM TIMES ta nemi ya bayar da hujja, Lai ya ki cewa komai.

A na sa bangaren, Atiku ya ragargaji gwamnatin Buhari da yin sakaci da kuma rashin iya aiki, ta yadda har Buhari ya kasa gargadin Lai dangane da irin sakin-bakin da ya ke yi, wanda Atiku ya ce barazana ne ga tsaron kasar nan.

Atiku ya ce har yanzu wasu baragurbi kuma dibgaggu na nan su na kitsa makarkashiya da sharri a kasar nan, a karshe domin su goga masa bakin fenti kuma su bata masa suna.

Daga karshe ya yi kira ga gwamnati ta maida hankali wajen tabbatar da tsaron al’ummar kasar nan, maimakon ta yi tsaye zororo ta bar manyan jami’an ta sun bar jaki su na dukan taiki.

Share.

game da Author