RASHIN TSARO: Akwai Sakkwatawa da Zamfarawa 15,000 masu gudun hijira a Nijar -NEMA

0

Hukumar Bada Agajin Gaggawa (NEMA), ta bayyana cewa a zaman yanzu akwai ‘yan jihar Zamfara da Sokoto sama da 15,000 da ke gudun hijira a cikin Jamhuriyar Nijar.

Shugaban NEMA na yankin Sokoto, Kofoworola Soleye ne ya bayyana haka jiya Alhamis a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, a lokacin da ake gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan dabarun shawo kan barkewar bala’i a cikin al’umma.

Soloye yay i tsinkayen cewa wannan adadi na sama da 15,000 duk an raba su da muhallin su ne daga cikin Kananan Hukumomin Isa da Sabon Birni a Jihar Sokoto da kuma Shinkafi da Zurmi daga cikin Jihar Zamfara.

Kashe-kashe, hare-hare da farmakin ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane tare da kone kauyuka ne ya haifar da wannan kwararar masu gudun hijira zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

Ya ce tuni jami’an NEMA sun je har sansanin su a Nijar din domin tantance yawan su da kuma irin halin da suke ciki, yadda za a gaggauta kai musu tallafin rage musu kuncin rayuwar da suke ciki.

Sarkin Anka na Jihar Zamfara, Attahiru Ahmad, ya kara jajjada hanyoyin da ya taba bayarwa na yadda za a dakile hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

Share.

game da Author