RAHOTON MUSAMMAN: Yadda Manoman Najeriya ke noman tufa a cikin mawuyacin yanayi

0

Wuri ko gonar da Samuel Okoli ke noman tufa, wato ‘apple’ a Kaduna, bai yi kama da wurin da ya dace a yi noman kayan marmari irin wannan ba.

Duk da haka kuwa bishiyoyin tufa din sun yi kore shar – duk da cewa ana kartsa rana, kuma ana tsakiyar ranin da sai kwanan ne aka ma fara samun ruwan sama jifa-jifa.

Maganar gaskiya, babu wanda zai iya tunanin cewa za a iya ririta noman ‘apple’ a yanayi mai tsandauri da rana da tsawon rani kamar a Kaduna.

Shi kan sa Okoli ya sha ji mutane na cewa ba zai yiwu a noma tufa, wato ‘apple’ a yanayi kamar irin na Kaduna ba.
Sai dai kuma ba kamar sauran mutane da suka yarda ta wannan maganar ba, shi kuwa Okoli sai ya dauki aniyar cewa zai jaraba ya gani, kuma ya jaraba din.

Da jarabawa kamar da wasa, sai ga Okoli, wanda ya mallaki shaidar digiri a fannin inginiyan kayan lantarki, ya fara noma tufa, wato apple gonar sa da ke bayan gidan sa a Kaduna.

Sai dai kuma ba tun yau ko bar Okoli ya far aba. Tunanin ya zo masa tun a cikin shekarar 200, bayan da ya ziyarci gonar Jarakanda, wadda ke kilomita 20 a wajen Kaduna. A can ne tunanin fara noma tufa ya zo masa. Ya ce a can ya sayi irin jan tufa na naira 8,000 duk daya, ya dauka ya kai ya shuka a cikin Kaduna.

“Na yi tunanin noman tufa, saboda shi ne kayan marmarin da kowane dan Najeriya ke son ya ci, kuma ana kashe makudan kudade wajen shigo da shi daga waje.

TUFA: Sai An Sha Wuya AKe Shan Dadi

Babu wanda zai taba tunanin cewa za a iya noma tufa, wato apple a gari kamar Kaduna mai zafin rana ma’aunin digiri 25.2 C a lokacin rani. Musamman idan yanayi ya kara yin zafin da ya kai har digiri 40. C.

Domin a dukkan fadin duniya, masana dabaru da ilmin noman tufa sun auna cewa sai dai kasa da digiri 21-24 C da kuma mai tsanani kasa da digiri 40.C.

Ya Injiniya Ya Jure Noman Tufa tsawon Shekaru 20?

Wannan kuwa babbar tambaya ce, amma bari ku ji daga bakin mai ita:

“Bayan na kawo irin na shuka, na farko da suka fito ba su yi kyau sosai ba. Amma a haka na rika kula da su. Har dai na fahimci ashe za su iya girma su zama bishiya sosai. Da farko na dauka kawai idan sun fito za su kama kamar haki, amma sai na fahimci za su iya girma su zama bishiyoyi.

“ Amma fa abu ne masu bukatar matukar kulawa sosai; sai ka rika kula da su, musamman sai ka yi da gaske idan wani ciwo ya kama su. Sai ka rika bas u ruwa, kuma ka na gyara su.”

“To sai kuma rani ya zo da wasu cututtuka. Na shuka guda 100, kamar guda 70 za su yi tsiro, sannan a cikin su din ma kashi 30 bisa 100 za su rayu.

“Saboda tsanannin zafi, tilas sai ka rika ba su ruwa. Amma ba ka da matsala a lokacin damina. Sai dai kuma za ka rika kula saboda kwari, tilas sai ka rika fesa maganin kwari.”

A yanzu dai Okoli ya yi karfi a noman tufa, har ya na saida iri a kan naira 10,000.00 zuwa 25,000.00.

SABON SALON NOMAN TUFA A JOS

Akwai wata gona a Jos, kilomita 200 daga Kaduna, inda ake noma kayan marmari a cikin Karamar Hukumar Jos ta Arewa. Sunan gonar Jamil Farm and Garden.

Sai dain ba kamar yanayin Kaduna ba, shi yanayin Jos ya na da kyau sosai, ta yadda Sadis Abbas ya yi nasarar gwajin na sa noman.

Abbas ya na da difloma a harshen Larabci, ya fara shuka tufa tun cikin 2010.

Shi din ma kamar Okoli, cewa ya yi zai jaraba domin ya nuna wa ‘yan Najeriya cewa za a iya noma tufa a nan Najeriya. Amma shi da koren tufa ya fara, ba da jan tufa ba.

A yau Abbas na da irin tufa kala-kala a cikin gonar sa, a tsawon shekaru 18 da ya yi ya na noman tufa.

“Na rika samunn irin tufa daga tufa din da kosa ya jama’a ba su sha’awar sayen sa, domin ya fi arha. Sai na tsaga shi gida biyu, na cire ‘ya’yan na shuka.

“Yanzu burin da na sa gaba shi ne na fito na nawa irin tufa din wanda zan sa wa suna Manzalia apple. Na tafa shuka nawa irin a baya, ba yanzu ne karon farko ba. Na sayar da na farkon ga wani malami da ke kwas din digirin-digirgir a kan tufa. Kuma mai lura da aikin na sa ya amince da shi hannu bib-biyu.”

Share.

game da Author