Yadda Gwamnonin Jahohi Ke Yi Wa Kananan Hukuma Mulkin Mallaka, Daga Kais Daud Sallau

0

Kananan hukumomi an kirkire su ne domin su samarwa al’umma da suke kauye da karkara saukin kai bukatun su zuwa ga gwamnatin jahar da na tarayya, domin samun cin gajiyar gwamnati cikin sauki ta hanyar shugaban karamar hukuma. Shugaban karamar hukuma tare da taimakawar wakilcin gunduma (councilor) sune tsani tsakanin gwamnatin jiha da al’ummar da su ke kauye ko karkara saboda nisan su da gwamnati.

Shuwagabannin kananan hukuma su suka fi sanin matsalolin al’umma, domin su ke tare da talakawa. Sune hukumomin gwamnati da talaka ke iya gani.

Kama daga gwamna zuwa shugaban kasa ba mutane ne wadanda ake ganin su cikin sauki ba. Kafin ka samu daman ganin gwamna ko shugaban kasa dole sai kai mai fada a ji ne, kokuma kana da alaka da wannan gwamnan ko shugaban kasa. Saboda da haka dole ta hanyar shugaban karamar hukuma gwamna zai san matsalar mutane da ke nesa da shi, shi kuma yaga shugaban kasa.

A baya zaka ga shugaban karamar hukuma na iya yi wa al’ummar shi aiki kama daga gina gota da gada, gina asibiti, gina makaranta, gina kasuwa, samar musu ingantaccen ruwa shan da sauran su. Amma yanzun zaka ga shugaban karamar hukuma zai hau mulki har ya sauka bazai yi wani aikin ko daya ba sakamakon mulkin mallaka da gwamnonin jahohi su ke yiwa kananan hukuma na sace kudaden kananan hukuma da gwamnatin tarayya su ke turo wa. Hakan ya taimaka gurin karancin ci gaba a matakin kananan hukuma, da kuma yawaitar rashin kudi.

Yadda Gwamnonin Jahohi Ke Yi Wa Kananan Hukuma Mulkin Mallaka

Gwamnonin jahohi sun mai da kananan hukuma gurin tatsan kudi, an kai matsayin da albashin ma’aikatan karamar hukuma gwamna ke biya ba shugaban karamar hukuma ba. Kawai shi shugaban karamar hukuma saide ya jira gwamna ya ba shi abinda da ya samu. Ba maganan tura mishi da kudin yi wa al’ummar shi aiki, kuma ba za su je su yi musu wani aiki ba.

Akasari idan kaji ance wannan gwamna yana aiki, toh duk bai wuce a cikin birnin jihar ya ke aiki ba, babu ruwan su da kananan hukumomin da suke karkashin. Su tsakanin su da kananan hukuma, su sace abinda gwamnatin tarayya ta ke turo musu duk wata.

Abinda ya sa gwamnoni baza su so a ce kananan hukuma sun samu ‘yancin kai ba shi ne, saboda kashi talatin da biyar (35%) cikin dari, koma sama da haka na kudaden da gwamnoni ke sacewa daga cikin kudaden kananan hukumomi ne da gwamnatin tarayya ke tura musu suke zantarewa ta hanyar asusun hadin kai tsakanin gwamnatin jihar da na kananan hukuma (Joint Account) saboda rashin imani da zalunci.

Ba wani abu a cikin asusun hadin kai na jiha da kananan hukuma (Joint Account) sai zalunci da sata. Da wannan asusu hadin kai ne gwamnonin jihohi su ke amfani su ke sace kudaden kananan hukuma. Misali idan ya kamata a turawa karamar hukuma naira miliyon hamsin (50m) ne, to, ta hanyar wannan asusun hadin kai na jiha da kananan hukuma (Joint Account) gwamna zai zaftare naira miliyon hamsin (50m) zuwa naira miliyon ashirin (20m), wannan ma a jihar da shuwagabannin kananan hukumomi su suke biyan albashin ma’aikatan karamin hukuma kenan ta hanyar biya a tebur (Table Payment). Amma a jihar da gwamnoni su ke biyan albashin ma’aikatan karamar hukuma ta hanyan banki (Bank Payment), toh bayan gwamna ya biya ma’aikatan karamar hukuma, sai de ya nima wani abin goro ya turawa shugaban karamin hukuma (Local Government Chairman). Kuma su shuwagabannin kananan hukumomin basu isa suyi magana ba saboda akasari hanyar da ake kawo su mulki akwai rashin adalci a ciki, ba zaban su a ka yi ba. Saboda haka dole su yi shiru.

Yana daya daga cikin mulkin mallakan da gwamnoni ke yi wa kananan hukuma kaga gwamna sai yayi shekaru uku da watanni kafin ya yi zaben kananan hukuma. Kawai gwamnati rikon kwarya su ke bayarwa domin su ji dadin kwashe kudin kananan hukumomin.

A cikin salon mulkin mallakan da gwamnoni ke yi wa kananan hukuma harda rashin biyan ma’aikatan kananan hukuma albashin. Akasari idan kaji ance gwamna bai biya ma’aikata albashi ba, toh zaka ga ma’aikatan karamar hukuma ne ba’a biya su ba, domin su ne wadanda gwamnoni su ka rena. Zaka ga gwamna yayi watanni shida koma fiye da haka baya biyan ma’aikatan kananan hukuma albashin su saboda zalunci da rashin imani. Bayan kowa yasan akasarin ma’aikatan karamar hukuma talakawa ne, kuma su ke tare da mafiyawan cin talakawa a karkashin su wadanda su suke daukar nauyin su kama daga ciyarwa, makaranta, kiwon lafiya da sauran su. Amma da yake su gwamnonin talaka ba shi ba ne a gaban su shiyasa su ke hana ma’aikatan albashin su, duk halin da zasu shiga su babu ruwan su.
Kais Daud Sallau.

Karin Karancin Albashi zuwa dubu talatin (30,000 Minimum Wage)

Yadda zaka kara ganewa cewa gwamnonin nan ba talakawa bane a gaban su, ka duka yadda su ke nuna bakin cikin su da adawa da karin albashi (Minimum Wage) wanda ake kokarin yi daga naira dubu goma sha takwas (18,000) zuwa dubu talatin (30,000). Wai saboda rashin imani wadansu gwamnonin wai basu da kudin da zasu biya wannan dubu talatin (30,000) na karamin albashi sai kace noma zasu yi su samo kudin. Wanda kowa yasan zuciyar su a mace ya ke, suma jira su ke daga gwamnatin tarayya a turo masu. Basu iya kirkiro yadda za su samo kudin shiga a jihar su ba, saide su jira a basu.

Kowa yasan yadda abubuwa suka kara kudi a kasan nan wanda duk mai imani ya san ma’aikata sun cancanci a kara musu albashi. Lokacin da ma’aikaci ya ke karbar dubu goma sha takwas (18,000) da yanzun kudin kaya ba daya ba ne. Amma wadansu gwamnoni saboda rashin tausayi suna bakin ciki da karin. Saboda sun san zai rage musu yawan kudaden da suke sacewa.

Su gwamnatin jihohin su zauna basu kirkiro hanyar shigowan kudi na matakin jihar (IGR) sun dogara ga kudin da gwamnatin tarayya su ke turawa saboda rashin kishi da son ci gaban jihar su. Shiyasa a ko da yaushe zaki ji su suna korafi cewa ba kudi, amma za ka gan su suna yin abubuwa na kudi idan wannan abin su zasu amfana da shi.

Toh Menene Mafita Game Da Lamarin Kananan Hukuma

Na farko,, kananan hukuma su samu yancin kansu wanda za’a dinga turo musu da kudaden na duk wata ba tare da ya bi ta hanun gwamna jiha ba. Ta nan ne suma shuwagabannin kananan hukuma zasu samu isassun kudaden da zasu yi wa al’umma aiki kamar yadda muka sani a baya.

Na biyu, samun yancin kai kananan hukuma na samun kudaden su daga gwamnatin tarayya kadai ba zai canza mulkin mallakan da gwamnoni ke yi wa kananan hukuma yadda ake so ba. Dole za’a yi doka wanda zai kasance zaben shuwagabannin kananan hukuma gwamnatin tarayya su zasu dinga gudanar da shi. Idan ba haka ba, toh kamar an kashe maciji ne ba’a yanke kan shi ba. Idan har ake ce za’a bar gwamnatin jihar su ci gaba da gudanar da zabukan kananan hukuma, toh ko tanan za’a ci gaba da tatse kudaden su. Domin gwamnoni zasu ci gaba da kawo yaran su, suna kwashe kudi suna kai mu, kokuma su ma ki yin zaben kamar yadda su ka saba. Saboda yan majalisun jahohi a aljuhun gwamnonin su ke, sai yadda su ka yi da su.

Na uku, dole kotur da za ta yi shari’ar zaben shuwagabannin kananan hukuma (Local Government Elections Tribunal) daga gwamnatin tarayya za’a kafa. Idan har za’a bar shi karkashin gwamnatin jiha, toh, tanan ma za’ayi abin da ake so.

Idan har za’a karbi wadannan abubuwa guda uku daga hanun gwamnatin jihar, toh da Ikon Allah talaka zai ga canji, kuma za’a samu ci gaba matuka a matakin kananan hukuma.

Daga karhe ina son ‘yan uwana talakawa su fahimci cewa, duk gwamna ko dan majalisar na tarayya ko jiha da baya goyon bayan samun yancin kai kananan hukuma, toh makiyin talaka ne.

Haka kuma duk gwamnan da baya goyon bayan karin albashi zuwa dubu talatin (30,0000 Minimum Wage) shima makiyin talakawa ne.

Saboda kashi tasa’in da biyar cikin dari (95%) na ma’aikatan karama hukuma talakawa ne. Babu yaron shugaban kasa, gwamna, Minista, ko komishina da yake aiki a karamar hukuma, kai ko shuwagabannin kananan hukuma ba kowa ya ke barin yaron shi yayi aiki a karamar hukumar ba.

Saboda haka duk wanda yayi adawa da samun yancin kananan hukuma da karin albashi zu dubu talatin, toh da talaka ya ke fada, mu shirya karan fadan mu, waton katin zabe (Voter’s Card) zuwa ranar zabe, sai mu nuna musu amfanin mu. Daman zaben 2023 iya ruwa fidda kai ne, kowa tashi ta fishe shi. Muna kallon iya takun kowa, katin zaben mu na ajiye. Ba suna ganin kamar suna da shekaru hudu ba, a gurin Allah kamar gobe ne.

A takaice wannan shi ne dan bayanin da zan yi akan yadda gwamnoni ke yi wa kananan hukuma mulki mallaka. Shiyasa ba za su goyi bayan shirin da a ke yi na zame su daga jikin su ba. Idan wani yaga abinda ya bata mishi rai yayi hakuri, idan anga kure, toh daman bamu fi karfin yin kuskure ba.

Allah ya ba mu zaman lafiya a kasar mu, ya ba mu damini mai albarka. Amen.

Share.

game da Author