Masu Garkuwa sun nemi a biya su Naira miliyan daya diyyan ma’aikatan FRSC da suka sace

0

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen jihar Osun (FRSC) ta bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da ma’aikatan hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa su biyu sun nemi a biya Naira Miliyan daya kudin diyyan su kafin su sake su.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda wasu masu garkuwa da mutane suka sace Bayegunmi da Abioye ma’aikatan FRSC a hanyar Iwaraja dake karamar hukumar Oriade ranan Litini.

Kakakin FRSC Bisi Kazeem da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Folashade Odoro suka tabbatar wa ‘yan jarida da haka.

A sako da ya aika wa manema Labarai ranar Talata Kazeem ya bayyana cewa maidakin daya daga cikin ma’aikacin da akayi garkuwa da da aka yi garkuwa da ta ce sun kira ta sannan sun bukaci a aika musu da Naira miliyan daya kafin su sake ta.

” Masu garkuwan sun bukaci da a biya wadannan kudade a yau Talata da karfe tara na safe.”

Garkuwa da mutane da karban kudaden diyya ya zama ruwan dare a Najeriya.

A cikin kwanakin nan ne wasu masu garkuwa da mutane suka saki wani farfesan jami’ar Awolowo dake Ile -Ife bayan an biya kudin diyyar sa.

Sannan a jihar Ekiti wasu masu garkuwa da mutane sun sace mutane uku ranan Lahadi inda suke bukatan a biya su kudin diya sama da Naira miliyan 20.

Share.

game da Author