Mahimman dalilan dake hana mata aure Arewacin Najeriya

0

Burin kowani uba ne ace yau ya wayi gari yaga ‘yarsa a dakin mijinta musamman a wannan yanki na Arewacin Najeriya. Hakan ba wai ya tsaya a Arewa bane kawai wannan burine na duka wani Uba da ya san ciwon kansa.

A da mace kan zama abin nunawa ga iyayenta, danginta da al’uma gaba daya idan har ta kai wani shekaru bata yi aure ba.

Abin ma har ya kan shafi zaurawa mata da matan da suka ki aure bayan mazajen su suka rasu.

A hiran da wasu mata suka yi da PREMIUM TIMES HAUSA matan sun bayyana cewa mata kan yi haka ne saboda su gujewa wulakncin maza da kuma wasu da dama kan ki yin aure ne saboda zama tantiriya wajen tambadewa.

Ga wasu hujojiin da suka bada;

1. Isa: Kamar yadda suka bayyana. Mata a wannan zamani suna son ace suma sai yadda suke so za ayi. Hakan yasa wasu da dama basu iya zama karkashin wani namiji da sunan wai a karkashin shi suke. Idan tana zamn kanta to zata yi abinda da take so babu mai takura mata.

2. Yaudara: Wasu matan kan fada tarkon mazaje masu yaudara. Idan har mace bata yi sa’an samun nagari ba sai kaga ta fada cikin irin wannan hali da hakan sai ya sa ayi ta fama da ita. Taki yi auren ko kuma ma sauraren wani namiji.

3. Son Abin Duniya: Son jin dadi da watayawa kan sa zaman aure ya gagari mata sau da yawa. Wasu matan kan su a yi ta jin dadi ne. Idan miji ya samu kararyar arziki shike nan sai ta yi ta dabalbale sa da fitina. Nayau dabam da na gobe. duk don ta samu damar sheke ayar ta a waje ta yi abin da taga dama.

4. Daidaita jinsin Mace da Namiji: Yanzu akwai kungiyoyi da suka fito suna kira ga mata da su nemi hakkin su a wajen mazajen su. Cewa daidai suke da maza. Idan Ta goya yaro shima gobe ya goya yaron Sannan ma su raba ranakun girki da wanke- wanke. Duka irin haka na dada rudin mata wajenkin zaman aure.

5. Banbancin addini: Wasu kuma a dalilin rashin zaman su a inuwar addini daya da wadanda suke so, hakan na sa su auren ma ya gagara. sai suga idan ba wanda suke so bane ba za su yi auren ba ma kawai.

6. Tsananin talauci da Dogon Buri: Wannan shima babban matsala ce da ake fana da shi a wannan zamani da muke ciki. Rashin abin hannu da kuma cika tumbi da aka yi da burin tsiya kan sa mata su ki yin auren kwata-kwata ko kuma ma da sun yi su ki zama.

Share.

game da Author