A yau Litinin fitaccen alkalin Babbar Kotun Tarayya a Abuja, Nnambi Dimgba, ya kori karar da EFCC ta maka Robert Azibaola, inda hukumar ta zarge shi da laifin lashe dala miliyan 40.
Da ya ke yanke hukunci a yau, Mai Shari’a Dimgba ya ce duk da an dade tsawon lokacin ana tafka wannan shari’a, EFCC ta kasa gabatar wa kotu kwararan hujojin da za su iya tabbatar da cewa Azibaola ya ci kudaden.
Ya ce kamata ya yi mai gabatar da kara ya gabatar masa da tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, Sambo Dasuki, a matsayin mai bayar da shaida.
“Tunda mai gabatar da kara ya kasa gabatar da shaida daga ofishin Mashawarci a Fannin Tsaro, babu wata hujjar da ke tabbatar da an bayar da kudi, kuma wanda ake zargi ya karba din.
HUKUNCIN MAI SHARI’A
“EFCC da mai gabatar da kara sun nuna azarbabin damuwa da shari’ar, fiye ma da wanda ake zargin an yi wa lafin (Gwamnatin Tarayya kenan).
“Sannan kuma mai gabatar da kara ya kasa tabbatar da hujjoji sahihai wadanda za a ce ga hujja ba wai zargi ba, a dukkan caje-caje guda biyun da suke yi wa wanda ake kara.”
“Don haka na sallami wanda ake kara, ya tashi ya tafi, an wanke shi, ba shi da laifi.” Inji Mai Shari’a Dimgba.
Idan za a iya tunawa, EFCC ta kama Azibaola, dan’uwan Jonathan, suka maka shi kotu tare da matar sa Stella da kamfanin sa.
KWATAGWANGWAMAR SHARI’A
An zargi sun karbi dala milyan 40 da sunan kwangila daga hannun Sambo Dasuki.
An gurfanar da su tun daga ranar 7 Ga Janairu, 2016, sannan aka karbi belin su a kan kowanen su naira milyan 500.
An sake maka su kotu a ranar 27 Ga Afrilu, 2017, a kan wasu tuhume-tuhume guda tara, wadanda da aka yi wa kwaskwarima daga na farko.
A yayin da aka dauki tsawon lokaci an tafka shari’a, mai gabatar da kara ya kira shaidu 10, tare kuma da damka wa kotu wasu takardu na shaidar asarkala ko sabarkalar kudade da ake zargin Azibaola, matar da Stella da kuma kamfaninn sa mai suna One Plus Company.
An tafka gurugubjin musayar yawun gabatar da hujjoji da kuma kare kai tsakanin lauyoyi masu gabatar da kara na EFCC da kuma lauyoyin su Azibaola, har dai daga baya aka umarci Azibaola da One Plus Company su kare kan su a zargi guda biyu.
Ita kuwa Stella matar sa, tuni aka cike sunan ta daga cikin wadanda ake tuhuma.
Azibaola ya ki amsa tuhumar karbar kudaden da EFCC ta ce ya karba, ya yi shagalin gaban kan sa da su.
Ranar 6 Ga Fabrairu, 2019 ne lauyoyin da ke kare Azibaola a karkashin babban lauya Chris Uche, suka shaida wa Mai Shari’a cewa sun kammala duk wani bayanin kare kan su a gaban kotu, za su jira hukunci.
Sun yi haka ne bayan sun kira wasu shaidu biyu, har da shi Azibaola din, kuma suka gabatar da takardun shaidun wanke kai masu dimbin yawa.