Buhari ya sa hannu a kan Kasafin 2019 na naira tiriliyan 8.9

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin naira tiriliyan 8.9 na 2019.

Tun daga yau 27 Ga Mayu, 2019, kasafin 2019 ya tabbata kuma ya zama a cikin doka kenan.

Ya sa wa kasafin hannu yau Litinin da karfe 11 na rana, a ofishin sa da ke Fadar Gwamnatin Tarayya, Aso Villa, Abuja.

Majalisar Dattawa da ta Tarayya ne suka amince da kasafin kuma suka mika masa domin ya sa masa hannu a zama doka.

Sun aika wa Shugaba Buhari kasafin bayan sun kara shi daga naira tiriliyan 8.826 suwa naira tiriliyan 8.916 a cikin watan Disamban 2018.
Majalisun sun yi wa kasafin karain naira bilyan 90 kenan.

Yayin da Buhari ke sa wa kasafin hannu, ya ce karin da Majalisun biyu suka yi wa kasafin zai shafi yadda za a aiwatar da shi, wajen gudanar da ayyuka.

Majalisun dai sun yi wa wasu bangarori karin kudi, yayin da kuma suka rage a wasu bangarorin.

Buhari ya sa kasafin hannu a gaban Kakakin Majalisa Yakubu Dogara, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu da kuma Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa a kan Kasafin Kudi, Sanata Danjuma Goje.

Daga baya Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya isa wurin a makare.

Share.

game da Author