Masu garkuwa sun yi awon gaba da matar malamin jami’a

0

Jiya Lahadi ne wasu ’yan bindiga suka sace matar wani malami a Jami’ar Niger Delta University, a Jihar Bayelsa.

Maharan sun shiga har yankin Gbaramboru da sassafe, suka gudu da ita, bayan da suka rika harba bindigogi a sama, domin su tarwatsa jama’a.

An ce sun shiga yankin ne ta yi amfani da kwale-kwale mai gudu ta hanyar Kogin Nun, inda suka isa gidan malamin jami’ar, wanda aka bayyana sunan sa Dakta Charles.

Wani dan garin wanda ya nemi a sakaya sunan sa, don gudun kada a dirar masa daga baya, ya ce masu garkuwar sun je ne da nufin kama malamin jami’ar ba matar sa ba. Amma sai ya tsere, suka kama matar, suka saka ta a cikin kwale-kwale, suka tsere da ita.

Matasan garin sun fito jim kadan bayan an arce da matar, inda bayan nan kuma sai ga malamin jami’ar ya fito daga inda gudu ya boye.

Kakakin ‘yan sandan jihar Bayelsa, Asinim Butswat, ya ce sun a sane da labarain an yi garkuwa da matar, kuma su na kan hanyar cimma wadanda suka gudu da ita.

Ya ce ba za su gajiya ba har sai sun cim musu, kuma sun ceto ta.

Share.

game da Author