DADDATSA MASARAUTAR KANO: Yunkurin kawo ci gaba ne ko bi-ta-da-kullin siyasa ne? Muhimman Tambayoyi 12

0

Gwmnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu Kano, bayan da Majalisar Dokokin Jihar ta mika masa dokar.

Tunda gwamna ya sa hannu, to zai kasance Masarautar Kano mai dimbin tarihi tun daga zamanin Bagauda, jikan Bayajidda wanda ya yi sarauta daga 999 zuwa 1063, za ta ragu ta koma Kananan Hukumomi 8 kawai, maimakon 44.

Shekaru 1020 kenan da kafa Masarautar Kano, amma Ganduje zai daddatsa ta kamar yankan sandar rake.

Kananan Hukumomin da za su rage a karkashin Kano, sun hada da: Municipal, Gwale, Dala, Ungogo, Fagge, Nassarawa, Kumbotso da kuma tarauni Tarauni da Dawakin Kudu.

Ana kokarin kirkiro Masarautun Gaya, Bichi, Rano da Gwarzo.

Daga Gaya har Bichi, Rano da Gwarzo, babu garin da ya kai girman unguwar Kubwa ko Maraba, Gwagwalada ko Zuba ko Lugbe da ke kewaye da Birnin Tarayya, Abuja.

Gwarzo ko Rano ko Gaya ko Bichi babu wadda ta kai garin Funtuwa yawa ko yawan jama’a balle kasuwar da jama’a ke hada-hada.

Garin Malumfashi da ke Jihar Katsina ya zarce garuruwan Gaya da Gwarzo da Rano da Gaya kwarjinin alamomin ci gaba. Shin nada musu Sarakuna zai inganta tattalin arzikin su?

Wani ko kwandon rogo ko dankali ko makani da dafa daga Rano, Gwarzo ko Bichi, sai ya kai shi Kano sannan zai iya karewa a rana daya.
Duk ma ba wannan ba. Ga wasu tambayoyi guda 10 da ya kamata masu karatu su yi musayar yawu a kan su:

MUHIMMAN TAMBAYOYI 10 DANGANE DA KANO

1 – Shin Shugaba Muhammadu Buhari ya san an sa gatari an yi wa Masarautar Kano datsar guduwar kifi kuwa?

2 – Ko zai yiwu a iya zartas da wannan hukuncin ba tare da sanin Buhari ba?

3 – Shin da amincewar Kanawa za a zartas da wannan hukunci?

4 – Shin wannan ce sakayyar da gwamnatin APC za ta yi wa Kano? Kuma shin dattatsa Kano ce ta sa Kanawa yi wa APC biyayyar rakumi-da-akala?

5 – Shin babu ruwan ’yan siyasa da tuntubar manyan attajirai da shugabannin Kano ne?

6 – Yunkurin kawo ci gaba ne ko bi-ta-da-kullin siyasa ne?

7 – Wace riba Gwamna Ganduje zai ci idan ya tarwatsa tarihin shekara 1120?

8 – Hadin kai daddatsa Kano zai haifar ko tarwatsa zamantakewa?

9 – Ko wannan ce hanyar inganta al’ummar Kano kuma ita ce hanyar magance dimbin matsalolin Kano?

10 – Tilas sai Gwamnatin Ganduje ta shiga harkokin sarautar gargajiya?

11 – Ko kuwa sarautar Sarkin Bichi Ganduje zai nema idan ya sauka daga gwamna?

12 – Su wane ne mashawartan Ganduje, kuma aikin da aka tura wakilai kenan su yi a majalisa?

Share.

game da Author