Shaidancin APC ya nunka na PDP sau 10 – Gwamna Okorocha

0

“ Shaidancin da na yi gudu a cikin jam’iyyar PDP har na guje ta na afka APC, bai kai kashi daya bisa 10 na shaidanci da rashin mutuncin da aka yi min a APC ba.”

Haka Gwamnan APC, Rochas Okorocha ya bayyana a wata sabuwar caccaka da ya yi wa shugabannin jam’iyyar APC na kasa.

Okorocha, wanda shi ne Gwamnan Imo, ya fita daga jam’iyyar da ya ci zaben gwamna cikin 2011, wato APGA, aka yi ‘maja’ da APGA, ANPP, ANC da CPC aka kafa APC a zaben 2015.

Gwamnan mai barin gado, ya na fama da kwatagwangwamar hana bayyana sakamakon zaben sa da kuma bas hi takardar shaidar yin nasara a zaben sanata da ya tsaya a zaben 2019.

Ya zargi shugaban jam’iyyar APC da wasu shugabannin jam’iyyar wadanda bai ambachi sunayen su ba, cewa su na hada baki da INEC domin a kashe kaifin alkiblar siyasar sa.

Cikin wadanda ya furta sunayen su din, har da Festus Okoye, wanda ya ce da shi ake amfani ake kitsawa da kulla masa sharri da tuggu.

Haka dai Okorocha ya furta, a wata ganawa da ya yi da manema labarai kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

Idan ba a manta ba, INEC ta bayyana cewa Okorocha ne ya lashe zaben sanata na Imo ta Kudu. Sai dai kuma a cikin kankaninn lokaci ya nuna cewa tilasta shi aka yi, don ya ga ba yadda zai yi ne, sai ya amince ya sanar cewa Okorocha din ne ya lashe zaben.

Hakan ya sa INEC kin kiran sa domin ta damka masa takardar shaidar nasarar lashe zabe.

Ya zargi shugaban INEC da hada baki da shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole wajen kin ba shi takardar shaida.

Duk da wannn korafi da ya ke yi , Okorocha ya ce ya nan a cikin APC bai kai ga ficewa ba tukunna.

BATAN BAKATANTAN

Gwamna Rochas Okorocha ya nemi tsaida surikin sa Mr. Nwosu takarar gwamna a karkashin APC, da nufin ya gaje shi, amma uwar jam’iyya ta hana shi takara.

Ya fusata ya koma wata jam’iyya, inda 0korocha ya daure masa gindi, sai dai kuma jam’iyyar PDP ta yi nasara a zaben gwamna na jihar Imo.

Yanzu tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya ne, Emeka Ihedioha gwamna mai jiran gado a jihar Imo.

Share.

game da Author