Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada gwamnan babban Bankin Najeriya, Godwin Emiefile Gwamnan Bankin a karo na biyu.
Hakan ya biyo bayan kammala wa’adin sa na farko ne wanda zai cika ranar 2 ga watan Yuni.
Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ne ya karanta wasikar neman haka a zauren majalisar wanda Buhari ya aiko majalisar.
Idan Majalisar ta tabbatar da nadin, Godwin Emiefile zai ci gaba da zama gwamnan Babban bankin Najeriya din ne har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.