An rantsar da Buhari, Osinbajo karo na biyu a matsayin Shugaban Kasa

0

An rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari karo na biyu a matsayin Shugaban Kasa.

An rantsar da shi ne a Dandalin Eagle Square, a Abuja babban birnin tarayya.

Rantsarwar da aka yi a yau Laraba, ba ta yi armashi ba, domin shugabannin kasashe da dama ba su halarta ba.

Haka kuma a nan cikin gida Najeriya, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo, duk ba su halarta ba.

Dama gwamnatin tarayya ta ce ba za a gudanar da shagulgula a yau ba, domin za a yi bikin Ranar Dimokradiyya a ranar 12 Ga Yuni.

A jihohi kuma ana can ana ci gaba da rantsar da gwamnoni bayan da suka karfi mulki daga hannun wadanda suka kammala wa’adin su, ko kuma wadanda aka kayar a zaben 2019.

Buhari ya kayar da dan takarar PDP, Atiku Abubakar, inda Buhari ya samu kuri’u 15,191,847, shi kuma Atiku ya samu 11,262,978.

Sai dai kuma Atiku ya ki amincewa da sakamakon zaben, inda tuni ya garzaya kotu ya maka INEC, APC da Buhari kotu.

Share.

game da Author